Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya harbo sabbin masu linzami daga Legas

Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya harbo sabbin masu linzami daga Legas

- Atiku Abubakar ya kushe salon mulkin gwamnati mai ci yanzu

- Yayi alkawarin kawar da rashin aikin yi da yunwa

- Yace yana nan akan bakan shi na siyar da masana'antun duk da suka kasa

Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya harbo sabbin masu linzami daga Legas

Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya harbo sabbin masu linzami daga Legas
Source: Facebook

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kushe gwamnati mai ci yanzu da kuma bayyana gwamnatin damokaradiyyar da zai kafa mutukar aka zabe shi a zabe mai zuwa.

Wazirin Adamawan ya lissafo dokoki masu amfani da zai tabbatar matukar aka zabe shi.

1. Zamu samar da aiyukan yi ga mutanen kasar nan kamar yanda kowa yasani cewa babu aikin yi wanda hakan ne yasa talauci yayi yawa.

2. Hadin kai tare da tsaro a kasar nan: rashin hadin kai shine tushen rashin zaman lafiya. A saboda hadin kai ne ake samun fadace fadacen addini da kabila.

3. Yaki da fatara da samar da abinci.

4. Gina kasar da take duban muhallin doka da fifita ta akan kowanne mutum: kundin tsarin mulki kasa kadai shine zai zamo tushen dokar kasa.

GA WANNAN: Dakatar da Alkalin Alkalai: Buhari yayi wa tayar wasu tsiraru faci ne suna tsaka da kissa

6. Zamuyi aiki da bangarori masu zaman kansu na kasar nan don gano hanyoyin rage yawan cin bashi, matsalar karbar ninkin haraji da kuma samar da hanyoyin cinikayya tsakanin mu da kasashen kettle.

7. Zamu yanta guraren tattalin arziki tare da siyarda duk wata ma'aikata da ta gaza.

8. Zamu habaka kananan sana'o'i don su samarwa mutane abin yi.

9. Zamu habaka fannin ilimi da kiwon lafiya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel