Rushewar rumfar kamfen: PDP tayi karin haske a kan abinda ya faru a Kebbi

Rushewar rumfar kamfen: PDP tayi karin haske a kan abinda ya faru a Kebbi

- Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP reshen jihar Kebbi ta ce babu wanda ya samu wani mummunan rauni sakamakon rushewar rumfar kamfen a jihar Kebbi

- Mai magana da yawun jam'iyyar na jihar, Mallam Ibrahim Omie ya ce an kuma bawa wadanda suka sami kananan raunin kulawa a asibiti

- Jam'iyyar ta ce abinda ya faru ba komi bane illa alama da ke nuna jam'iyyar tana da dimbin magoya baya a jihar ta Kebbi

Mai magana da yawun jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, reshen jihar Kebbi, Mallam Ibrahim Omie ya ce babu wanda ya samu wani mummunan rauni sakamakon rushewar dandali da ya faru a wurin kamfen kwanakin baya a jihar.

Rushewar rumfar kamfen: PDP tayi karin haske a kan abinda ya faru a Kebbi

Rushewar rumfar kamfen: PDP tayi karin haske a kan abinda ya faru a Kebbi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zabe: Bai kamata a bari APC ta tsayar da 'yan takara a Zamfara ba - Sanatan APC

Rumfar kamfen din ya rushe ne a wurin taron yakin neman zaben PDP da akayi a Jega a jihar Kebbi yayinda Alhaji Abubakar Malam, mataimakin dan takarar gwamna na jihar ya ke jawabinda tare da magoya bayansa.

Omie ya ce wadanda suka samu kananan rauni sun samu kulawar likitoci a asibiti.

A cewar Daily Trust, mutane biyu ne suka samu rauni kuma aka garzaya da su asbiti. Faifan bidiyon rushewar rumfar dai tuni ya watsu a kafafen sada zumunta da kafafen yada labarai.

Wata sanarwa da aka danganta ga Ciyaman din PDP na jihar Kebbi, Mallam Haruna B. Sa'idu ya janyo hankalin mutane kan wani bidiyo da ya yi ikirarin APC da magoya bayanta ne su kayi kwaskwarima a akan rushewar rumfar.

Ya ce abinda ya faru ba wani abu bane illa tsabar kauna da goyon baya da al'ummar jihar Kebbi ke nunawa 'yan takarar jam'iyyar ta PDP musamman dan takarar gwamna, Sanata Isah Galaudu Augie.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel