Ganduje: Kotun Shari'a tayi watsi da karar da aka shigar a kan Jaafar Jaafar

Ganduje: Kotun Shari'a tayi watsi da karar da aka shigar a kan Jaafar Jaafar

- Kotun Shari'a a jihar Kano tayi watsi da karar da wani Dalhatu Shehu ya shigar a kan Jaafar Jaafar bisa wallafa faya-fayen bidiyon Gwamna Abdullahi Ganduje

- Dalhatu Shehu ya shigar da karar ne inda ya ke nema Jaafar Jaafar ya biya Naira Biliyan 3 a kan abinda ya kira bidiyon karya da aka wallafa domin cin mutuncin Gwamna Ganduje

- Sai dai daga bisani Dalhatu Shehu ya janye karar wadda hakan yasa Alkalin kotun, Mohammed Kademi ya yi watsi da karar

Wata babban kotun Shari'a da ke zamanta a Goron Dutse a jihar Kano tayi watsi da karar da wani Dalhatu Shehu ya shigar a gabanta inda ya ke neman babban Editan Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya gurfana a gaban kotun a kan wallafa bidiyon da ake zargin rashawa Gwamna Abdullahi Ganduje ya ke karba.

Ganduje: Kotun Shari'a tayi watsi da karar da aka shigar a kan Jaafar Jaafar
Ganduje: Kotun Shari'a tayi watsi da karar da aka shigar a kan Jaafar Jaafar
Asali: Twitter

A watan Oktoban 2018 ne Daily Nigerian ta wallafa wasu faya-fayen bidiyo da ke ake ikirarin Gwamna Ganduje ne ke karbar cin hanci na daloli daga hannun wani dan kwangila.

DUBA WANNAN: NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan Muhammad da Onnoghen

A Nuwamban 2018 ne Ganduje ya shigar Jaafar Jaafar kara inda ya ke neman a biya shi Naira Bilyan 3 saboda wai 'yadda bidiyon karya da niyyar cin mutuncin gwamnan da bata masa suna.

Duk da cewa Gwamnan ya shigar da kara a babban kotun da ke jihar, wani lauya da ke biyaya ga Ganduje mai suna Dalhatu Shehu ya shigar da wata karar a babban kotun Shari'ar a makon da ta gabata.

Da farko wanda ya shigar da karar ya ce akwai bukatar Jaafar ya gurfana a gaban kotun ya yi rantsuwa da Alkur'ani mai girma a ranar 29 ga watan Janairu.

Amma a lokacin sauraron karar ya yi a ranar Talara, Alkalin kotun, Mohammed Kademi ya yi watsi da karar inda ya ce wanda ya shigar da karar ya janye.

Lauya mai kare Jaafar, Audu Bulama-Bukarti ya nemi kotu ta bashi cikaken bayanin yadda aka janye karar kuma kotun ta amsa wannan roko nasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel