Masu garkuwa da mutane sun sace amarya da mata masu jego a Zamfara

Masu garkuwa da mutane sun sace amarya da mata masu jego a Zamfara

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara inda suka sace fiye da mutane 12 a ranar Litinin.

Wadanda aka sace sun hada da wata amarya da kuma wasu mata masu jego. 'Yan bindigan sun kai farmakin ne misalin karfe 11.45 na dare.

Mazauna garin sun ce 'yan bindigan sun rika harbe-harbe a iska wadda hakan ya razana mutanen garin.

Falalu Ashafa, malami a makarantar sakandire na mata da ke Zurmi ya ce matarsa,mahaifiyarsa, yaransa biyu da mai kula da yaransa suna cikin wadanda 'yan bindigan suka sace a harin na ranar Litinin.

Masu garkuwa da mutane sun sace amarya da mata masu jego a Zamfara

Masu garkuwa da mutane sun sace amarya da mata masu jego a Zamfara
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kamfen: APC ta bawa gwamnan da aka tura gidan yari mukami

Ana cigaba da kashe-kashen mutane da garkuwa da su duk da tsaurara matakan tsaro da gwamnati tayi har ma da canjin kwamishinan 'yan sanda na jihar.

Da aka tuntube shi domin samun bayani, Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya ce 'yan sandan sun fatattaki 'yan bindigan da su kayi yunkurin kai hari a daren Litinin amma daga baya suka gano an sace mutane 13.

Ya ce 'yan bindigan sun kai hari a garin Majema da ke Zurmi domin su tayar da tarzoma da hankulan al'umma ne.

"Amma hukumomin tsaro na hadin gwiwa da suka kunshi 'yan sanda, sojoji da 'yan kato da gora da ke Zurmi sun dakile harin nan take wadda hakan yasa 'yan bidigan suka koma cikin daji amma daga bisani aka gano sun sace mutane 13.

"Rundunar ta ce ta baza jami'anta domin bin sahun 'yan bindigan da niyyar ceto wadanda aka sace.

"Za mu cigaba da bawa 'yan jarida bayanin yadda al'amarin ke tafiya.

"Rundunar 'yan sandan tayi kira ga al'umma su cigaba da bayar da hadin kai ga 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro ta hanyar basu bayanai masu amfani a kan miyagun mutane da ke adabar jihar a kan lokaci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel