Yakin Neman Zabe: Jami'an tsaro sun shirya tarbar Buhari a jihar Kano

Yakin Neman Zabe: Jami'an tsaro sun shirya tarbar Buhari a jihar Kano

A yayin da guguwar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa ta jam'iyyar APC ke ci gaba da kadawa, an bayyana ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Kano domin girgiza magoya bayan sa.

Mun samu rahoton cewa, yayin da guguwar yakin neman zabe ke ci gaba da kadawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 31 ga watan Janairu, zai ziyarci jihar Kano domin girgiza magoya bayan sa yayin da babban zaben kasa ya gabato.

Wannan babban lamari ya sanya hukumar jami'an tsaro ta 'yan sanda reshen jihar ta bayyana shiri da daurin damarar ta na tarbar shugaba Buhari yayin ziyarar sa ta jibi. Hukumar ta sha alwashin tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya ga al'ummar jihar.

Yakin Neman Zabe: Jami'an tsaro sun shirya tarbar Buhari a jihar Kano
Yakin Neman Zabe: Jami'an tsaro sun shirya tarbar Buhari a jihar Kano
Asali: Facebook

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Abdullahi Haruna, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a Yammacin jiya na Litinin kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito.

DSP Haruna ya ce hukumar ta shimfida matakai tare da tanadi na jami'an tsaro domin tabbatar da yalwataccen tsaro da zaman lafiya gami da kwanciyar hankalin al'umma yayin babban taron na shugaba Buhari.

Babban jami'in ya kara da cewa, hukumar 'yan sanda za ta hada karfi da karfe da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da gudanar taron cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da wata tangarda ba.

KARANTA KUMA: Jonathan ya yabawa Gwamna Dickson yayin cikar sa shekaru 53 a duniya

A yayin da kawowa yanzu ba bu wani tabbaci na ziyarar shugaba Buhari, ana ci gaba da yada rahoton zuwan sa Kano a ranar Alhamis. Hakan ya sanya hukumar 'yan sanda ta gindaya jami'an ta shinge bayan shinge a wurare daban-daban da ke birnin Kanon Dabo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, ana sa ran shugaban kasa Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyyar sa ta APC za su halarci wannan babban taro a jihar Kano da ta kasance daya daga cikin jihohin Najeriya mafi yalwar al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel