Rundunar Soji ta tura gwarazan yan mata filin daga domin fafatawa da Boko Haram

Rundunar Soji ta tura gwarazan yan mata filin daga domin fafatawa da Boko Haram

Rundunar Sojin sama ta Najeriya ta aika da wasu sabbin kwararrun dakarunta yan mata zuwa filin daga domin su fafata tare da gwabzawa da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a yankin Arewacin Najeriya, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban hafsan rundunar Sojin sama, Sadique Abubakar ya bayyana cewa akwai Sojoji mata da dama dake bada gudunmuwa a matakai daban daban na yaki da yan ta’addan Boko Haram.

KU KARANTA; Samun tagomashi: Jam’iyyu 34 sun yanke hukuncin mara ma Atiku baya a 2019

Rundunar Soji ta tura gwarazan yan mata filin daga domin fafatawa da Boko Haram
Sojoji
Asali: UGC

Sadique ya bayyana cewa sun yi haka ne domin baiwa Sojoji daman cimma burukansu tare da gwada kwanjinsu ba tare da an nuna bambamci tsakanin mace ko namiji ba.

“Kamar yadda Sojoji maza suke bada gudunmuwa, hakanan su ma Sojoji mata suke bada gudunmuwa musamman wajen karkashe mayakan Boko Haram, muna kiransu ‘Matan Yaki’, kuma sun samu cikakken horon yadda zasu fuskanci abokan gaba.

“Sojoji mata sun kai hare hare da jiragen yaki kamar yadda mazan suke yi, sa’annan suna baiwa Sojojin dake kai samame a kasa kariya daga hare haren makiya, kamar yadda Sojoji maza ke yi, yawancin matan sun samu horo a kasashen waje, kuma sun tuka jirgin Beechcraft, wanda ake amfani dashi wajen tattara bayanai, shawagi da kuma sinitiri a sararin samaniya.

“A yan kwanakin da suka gabata ma sun taimaka ta hanyar yin shawagi a sararin samaniyar yankin Arewa maso gabas, musamman a jahar Borno da yankin tafkin Chadi, inda suka gano sansanonin yan ta’adda, tare da antaya musu ruwan wuta ba kakkautawa.” Inji shi.

Daga karshe rahotanni sun tabbatar da cewa akwai wasu Sojoji mata da dama dake samun horaswa a kasashen duniya daban daban don kara samun gogewa da sanin makaman aiki, akwai guda dake samun horo a Amurka akan yadda ake sarrafa jirgin yaki na musamman, wata kuma a Afirka ta kudu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel