Wasikar PDP ga duniya: Shugaba Buhari na shirin juyin mulki ta hanyar Kotun Qoli

Wasikar PDP ga duniya: Shugaba Buhari na shirin juyin mulki ta hanyar Kotun Qoli

- Ana zargin Buhari da kokarin sauke na biyar a kasar nan

- Mabiyansa sun ce bai ma sani ba

- An sami makudan kudade a asusun shugaban Kotunan

Wasikar PDP ga duniya: Shugaba Buhari na shirin juyin mulki ta hanyar Kotun Qoli

Wasikar PDP ga duniya: Shugaba Buhari na shirin juyin mulki ta hanyar Kotun Qoli
Source: Depositphotos

Bayan da aka ga kudi a asusun shugaban Alkalan kasar nan, alkalin alkalai Jastis Onnoghen Walter, wanda ya fito daga Neja Delta, an kai shi kotun CCT, lamari da ya dugunzuma bangaren sharia na kasar nan, ana dab da shiga zabuka.

Yanzu dai PDP ta saki martani a shafinta na Facebook kamar haka:

Muna kira da babbar murya da Majalisu na kasa, Amurka, Turai, da Ingila da su sanya masa takunkumi muddin ya iyar da nufinsa na kwatar kotu zuwa karkashinsa.

Mu PDP, munyi amanna har yanzu Cif Jastis Walter Onnoghen shine shugaban kotunan Najeriya, don haka bamu yarda da yadda shugaba Buharii ke kokarin dora sabon Alkalin Alkalai na kasa ba da ma rantsar dashi.

GA WANNAN: INEC ta kuma yin warwatsi da wani dan takarar APC bayan na jihar Ribas

Bamu yarda ba, ba kuma zamu yarda ba, shugaba Buhari ya maida mu zamanin mulkin soja ba, ko kuma ya komar da Najeriya tashi ta kama karya.

ahimtar ba zai ci zabe bace ta sanya ya koma karfa karfa, to lallai shugaba Buhari ya kula kada ya jefa kasar nan cikin tashin hankali, kan kokarin sai ya kwace majalisu da kotuna daga hannun gwamnati da jama'a.

Babu yadda za'a yi ayi shugaban Alkalai har biyu a kasa daya, shugaba Buhari kuma ya dora sabon alkalin alkalai ya lika wa wancan na gaskiyar kashin kaji, wannan baza ta sabu ba. Ba zamu yarda ba, muna kira ga 'yan Najeriya da kada su sake su yarda.

Muna kira da babbar murya, lallai 'yan Najeriya su fito, su nuna basu yarda APC ta kwace majalisa ta mika wa Buhari ba, ko kuma ta mika masa Kotunan kasar nan, wannan ba zata sabu ba, kuma ba zai yiwu ba.

Muna kira a karshe, dole a koma da zaman da majalisu suka daukarwa hutu, su dauki babban mataki kan Buhari kafin ya kwace kasar nan da ma dimokuradiyyarta kamar yadda ya saba a baya.

Sa Hannun:

Kola Ologbonndiyan,

Jami'in yada labarai na PDP

Kuma sakataren PPCO na kasa, da sunan uwar jam'iyya PDP.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel