Tsugunne bata qare ba, inji NLC, duk da cewa manyan Janar din Najeriya sun tantance

Tsugunne bata qare ba, inji NLC, duk da cewa manyan Janar din Najeriya sun tantance

- Kungiyar kwadago ta yanke hukunci saka majalisar dattawa akan rage karancin albashi

- Kungiyar tace resunanta na jiha da tarayya shirye suke idan akan ki yin abinda suke so

- An taka ka'idar fitar da karancin albashi kamar yanda kungiyar kwadago ta duniya ta tanadar

Tsugunne bata qare ba, inji NLC, duk da cewa manyan Janar din Najeriya sun tantance
Tsugunne bata qare ba, inji NLC, duk da cewa manyan Janar din Najeriya sun tantance
Asali: UGC

A ranar juma'a ce kungiyar kwadago ta Najeriya ta tashi daga taron gaggawa na CWC da yanke hukuncin saka majalisar dattawa akan 27,000 na karancin albashi da fadar shugaban kasa ta mika musu a ranar laraba.

Shugaban NLC da yayi magana da muryar Najeriya bayan taron, Ayuba Wabba yace yanke shawarar na daya daga cikin hanyoyin da kungiyar kwadago ta shirya don tabbatar da gwamnatin ta mutunta tare da tabbatar da 30,000 a matsayin karancin albashi kamar yanda kwamitin da ta duba ta amince.

Yace duk bangarorin ta na matakin jiha da tarayya ta sanar dasu akan su shirya don yajin aiki in har majalisar dattawan taki fitar da sakamakon da suke so.

A ranar talata, a taron NCS an amince da 27,000 a matsayin karancin albashin ma'aikatan Najeriya akan 30,000 da akayi ciniki akan ta wanda kwamitin ta mikawa gwamnatin tarayya.

Wabba yace CWC sun ki amincewa da 27,000 da NCS ta amince da kuma a shirye suke da su hada da majalisar dattawa a ranar litinin.

"Bai yi daidai ba ace za a rage kudin har zuwa 27,000 kuma ba tare da bin ka'idar da ta dace ba. Kamar yanda taron kungiyar kwadago ta duniya tace, tunda kwamitin majalisar dattawa suka amince da 30,000 din, babu wanda ya isa ya canza ta ba tare da bin ka'idojin da suka dace ba. Gwamnati a matsayin mai daukar aiki bazata iya ita kadai ta canza yawan kudin ba. Wannan maganar doka da ka'ida ce. A don haka ne CWC ta nuna rashin jin dadin ta tare da kin amincewa da rage yawan karancin albashin. Muna nan kan bakan mu akan abinda kwamitin majalisar dattawa ta yarje da ita."

GA WANNAN: An sace dan takarar APC anyi garkuwa dashi a jihar Edo, sun kashe mai tsaro nai

"Zamu shigo da yan kungiyar mu da majalisar dattawa akan maganar. Dole ne a mutunta cinikin mu kuma majalisar dattawa tayi abinda ya dace. Mun sanar da yan kungiyar mu abin yi idan ba ayi abinda ya dace ba. Tabbas zamu dau matakin da zai kare ra'ayin mu," inji shi.

CWC ta amince a ranar litinin zata saka majalisar wakilan a cikin maganar yayin jin karanta sabuwar dokar ga majalisar don tabbatar da anyi abinda ya dace.

Shugaban kungiyar kwadagon tayi alkawarin cewa zata fito don sanar da mtasayar ta don yan Najeriya su sani da ma duniya baki daya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel