Matsalar Tsaro: 'Yan Kamaru 32,000 sun fado Najeriya gudun hijira

Matsalar Tsaro: 'Yan Kamaru 32,000 sun fado Najeriya gudun hijira

- 'Yan gudun hijira dubu talatin da biyu ne daga kasar Kamaru suke neman mafaka a Nigeria

- Akalla 'yan kasar Kamaru 437,000 ne suka bat gidajen su

- Dubbunnan 'yan kamaru suna bukatar kulawa da tallafi

Matsalar Tsaro: 'Yan Kamaru 32,000 sun fado Najeriya gudun hijira
Matsalar Tsaro: 'Yan Kamaru 32,000 sun fado Najeriya gudun hijira
Asali: UGC

Majalisar dinkin duniya tace akalla mutane 32,000 ne suke neman mafaka a Nigeria daga kasar Kamaru saboda dalili na rashin tsaro da tashe tashen hankula.

Wakiliyar majalisar dinki duniya ta kamarun Mrs Allegra Baiocchi ce ta bayyana hakan. Baiocchi da shugaban kungiyoyin kariya ta kasar Mrs Yap Mariatou sunyi gargadin cewa akwai bukatar duba al'amarin na kasar ta kamaru domin ganin halin da jama'ar suke ciki.

Bayani daga majalisar dinkin duniya ya ce kasan mutane sama da miliyan hudu yan kamarun suke da bukatar tallafi Wanda yawancin su mata ne da kananan yara a dalilin haka sama da mutane dubu talatin da biyu ne suke neman mafaka a kasar Nigeria.

GA WANNAN: Wasu hadakar kungiyoyi na son a hana Obasanjo zuwa kasashen waje bayan zabe

Nigeria dai tana fama da matsalar tsaro musamman a bangaren area maso gabas domin kuwa fiye da mutane 10,000 suke yi gudun hijira daga Nigeria zuwa kasar kamaru a shekarar 2018.

Mrs Baiocci tace rashin tsaro da kuma hare haren da ake kaiwa a kasar kamarun yana karuwa a kullun amma ba a maida hankali a kan lamarin sannan wadanda abun ya shafa basa samun tallafi saboda haka yanzu tana ganin lokacin yayi da za a maida hankali wajen shawo kan matsalar.

Mariatou ma ta kara da cewa gwamnatin Kamaru itace ke da alhakin kare rayuwar mutanen kasar da dukiyoyin su saboda haka dole ta maida hankali wajen shawo kan matsalar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel