INEC ta kuma yin warwatsi da wani dan takarar APC bayan na jihar Ribas

INEC ta kuma yin warwatsi da wani dan takarar APC bayan na jihar Ribas

- Hukumar zabe ta kasa tace ba ruwanta da dan takarar da baya jerin sunayen da ta saki, tace dan majalisa Adebutu na jihar Ogun baya cikin jerin yan takarar

- Zatayi yaki da masu siyan kuri'a

- Jama'ar da zasu fito zabe a 2019 zasu fi na 2015 yawa

INEC ta kuma yin warwatsi da wani dan takarar APC bayan na jihar Ribas
INEC ta kuma yin warwatsi da wani dan takarar APC bayan na jihar Ribas
Asali: UGC

Hukumar zabe ta kasa tace duk dan takarar PDP da baya cikin jerin yan takarar da ta saki a garin Ogun to ya daina wahalar da kanshi da yakin neman zabe domin kuwa hukumar babu ruwanta dashi.

Mr Festus Okoye Wanda shine mai kula da sashin yada labarai na hukumar ya fadi hakan a gidan rediyon Rock city dake jihar Ogun.

Mr oladipupo Adebutu Wanda dan majalisar ne a jihar Ogun ya cigaba da yakin neman zaben sa tare da magoya bayansa duk kuwa da cewa baya cikin jerin sunayen da hukumar zaben ta saki.

Mr Okoye yace su fa da iya sunayen da jam'iyar PDP ta basu zasuyi amfani kuma mun saki sunayen a dokance duk wani Wanda baya cikin sunayen kuwa basu san shi a cikin yar takarar ba.

GA WANNAN: Alwalarka ta karye - PDP ga Buhari

Mr Okoye ya kuma kara da bayani akan masu siyen kuri'a a lokacin zabe in da yace suna nan suna aiki da jami'an tsaro domin ganin sun dakile wannan mummunar dabi'a. Yace duk Wanda suka kama a ranar zabe yana siyen kuri'a to zasu kame shu kuma zai fuskanci fushin hukuma.

Zaben 2019 dai zai kasance zaben da zaifi mafi yawan mutane da zasu kada kuri'a duba da yawan mutanen da akayi wa rijista Wanda zasu kai kimamin miliyan 80, sannan yan jam'iyu suna kara wayar da magoya bayan su domin su fito su yi zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel