Manyan illoli 2 dake tattare da man sauya launin fata da yan mata ke amfani dasu

Manyan illoli 2 dake tattare da man sauya launin fata da yan mata ke amfani dasu

Hukumar kula da ingancin kayan abinci da kwayoyi ta kasa, NAFDAC, ta gargadi yan Najeriya dasu guji amfani da mai ko kayan shafe shafe masu sauya launin fatan dan adam daga baki zuwa fari, saboda wasu manyan illoli guda biyu dake tattare dasu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye ne tayi wannan kira a ranar Alhamis a yayin da take ganawa da manema labaru, inda tace amfani da man sauya lauyin fata na haifar da cutar koda da kansar fata ga jikin dan adam.

KU KARANTA: Yansanda sun kama mutumin daya kashe matarsa, yayansa 2 da mutane 5 a Ebonyi

Manyan illoli 2 dake tattare da man sauya launin fata da yan mata ke amfani dasu
Bilicin
Asali: Twitter

Farfesa Moji tace ta ga dacewar yin wannan jan hankali ne duba da yadda hukumar NAFDAC ta kama wasu dimbin sinadaran hada mai masu canza lauya launin fata, da wasu yan kasuwa suka shigo dasu a jahar Legas.

“Akwai mutane da dama dake da hannu cikin badakalar shigo da ababen sauya lauyin fata, tun daga allurar glutathione, zuwa kwayoyi da sauran sinadaran canjin launin fata, domin kuwa a sati data gabata muka samu labarin wasu mutane sun baje hajarsu a kasuwar baje koli ta jahar Legas.

“Nan da nan jami’anmu suka yi ma kasuwar dirar mikiya, inda muka motoci dauke da allurar glutathione, mun fi damuwa da glutathione ne saboda babu abinda ya kaishi hadari a tsakanin ire iren sinadaran launin fata, yana janyo cutar kansar fata ya kuma lalata kodar dan Adam.

“Ya kamata jama’a su daina canza halittar Allah, mu kasance masu alfahari da bakar fatan da Allah Ya yi mu da ita, don haka mu a NAFDAC ba zamu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin mun kama duk ire iren haramtattun kayan da aka shigo dasu Najeriya.” Inji ta.

Daga karshe tayi kira ga yan kasuwa masu cinikin halastattun kaya dasu tabbata sun kai kayan nasu gaban hukumar domin tabbatar da an yi musu rajista, kuma an tabbatar da ingancinsu, ta yadda ba zasu cutar da yan kasa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel