Zan magance matsalar wutan lantarki kafin shekara daya - Dan takarar shugaban kasa

Zan magance matsalar wutan lantarki kafin shekara daya - Dan takarar shugaban kasa

- Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore ya ce zai iya magance matsalar wutar lantarki a Najeriya a kasa da shekara daya

- Dan takarar shugaban kasan ya yi wannan jawabin ne a wurin taron ganawa da tattauna na 'yan takarar shugaban kasa da ake gudanarwa a yau

- Sowore ya ce zai mayar da hankali ne wurin amfani da fasahar samar da lantarki da hasken rana domin kawo karshen matsalar wutan

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore ya ce ba zai cika shekara guda ba a kan mulki zai magance matsalar wutar lantarki a Najeriya idan har aka zabe shi a matayin shugaban kasa.

Ya yi wannan jawabin ne a yayin a wurin wani taron ganawa da tattaunawa da aka shirya domin 'yan takarar shugabanin kasa da Kadaria Ahmed ta shirya tare da tallafin gidan talabijin na kasa NTA da taimakon MacArthur Foundation.

Zan magance matsalar wutar lantarki cikin shekara daya - Dan takarar shugaban kasa
Zan magance matsalar wutar lantarki cikin shekara daya - Dan takarar shugaban kasa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya sake samun nasara a kan 'yan sanda a gaban Kotu

A yayin da ya ke magana a kan sauye-sauyen da zai kawo a fanin samar da wutar lantarki, Sowore ya ce: "Muna magana ne a akan mayar da hankali a kan fasahar samar da lantarki ta hanyar amfani da hasken rana (solar) da zai samar da 4,500 mega watt na wuta. Ko wace jami'a na bukatar 90 kilo watt sannan zamu gina tashohin samar da solar a sassan kasar. Zamu kammala kafin shekara daya.

"Kasar Masar sun samar da 14,000 mega watt a kan kudi N500,000 duk mega watt. Shine mafi araha a duniya. Za mu iya samar da shi a kasa da haka ma a Najeriya saboda muna da ma'aikata masu yawa.

"Abinda kamfanin Siemens ta so tayi kenan a Najeriya amma sai muka ce sai sun bayar da cin hanci hakan yasa suka tafi wurin wani kamfanin samar da lantarki na Masar mai suna RASCOM. Wannan abin kowa ya san da shi. Muna bukatar shugabanni na nagari. Bamu dashi, wanna shine matsalar. Muna bukatar sabbin dabaru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel