An yiwa shugaba Buhari nadin sarauta ta 'Sadauki Gwandu' a jihar Kebbi

An yiwa shugaba Buhari nadin sarauta ta 'Sadauki Gwandu' a jihar Kebbi

A yammacin yau na Laraba da Hausawa kan ce ma ta Tabawa ranar samu, hakan kuwa ta kasance ga dan asalin kasar Najeriya lamba daya wato shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya samu karamci da martaba ta nadin sarauta a jihar Kebbi.

Shugaba Buhari a fadar Mai martaba Sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar
Shugaba Buhari a fadar Mai martaba Sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar
Asali: Depositphotos

Shugaba Buhari a fadar Mai martaba Sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar
Shugaba Buhari a fadar Mai martaba Sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar
Asali: Facebook

Shugaba Buhari a fadar Mai martaba Sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar
Shugaba Buhari a fadar Mai martaba Sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar
Asali: Facebook

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a yau Laraba an rataya wa shugaban kasa Muhammadu Buhari martaba ta sarautar gargajiya a jihar Kebbi, inda aka ba shi rawanin Sadauki Gwandu, karamcin da ake yiwa Jaruman Sadaukai.

Sarkin garin Gwandi kuma jagoran masarautar jihar Kebbi baki daya, Alhaji Muhammadu Bashar, shine ya yiwa shugaba Buhari wannan rawani na karamci yayin dirar sa cikin jihar a Yammacin yau na Laraba.

Cikin majalisar Sarakunan gargajiya na jihar, Sarki Bashar da ya kasance wadanda suka fafata a yayin basasa kafada da kafada tare da Buhari, ya ce shugaban kasar ya cancanci rawani Sadauki Gwandu domin yabawa kyakkyawar nagarta, kwazo da kuma jarumta a bisa kujerar mulki.

KARANTA KUMA: A gabatar da Gana a matsayin dan takara - Matasan jam'iyyar SDP sun bayar da wa'adi kwana daya ga Falae

Yayin hikaito yadda suka fafata tare da aiwatar da bakin gumurzu a fagen fama na yakin basasa, Sarki Bashar ya ce shugaban kasa Buhari matabbaci ne kan duk wata sadaukar wa domin samar da ci gaba da kyakkyawar makoma ga kasar Najeriya.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya ziyarci jihar Kebbi a Yammacin yau bayan halartar taron yakin neman zaben sa da aka gudanar a Birnin Shehu domin neman goyon bayan al'umma yayin da ya rage sauran kwanaki kalilan a gudanar da babban zabe na kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng