Cakwakiya: Mata ta tayi aure alhalin muna tare - Miji ya shaida wa kotu

Cakwakiya: Mata ta tayi aure alhalin muna tare - Miji ya shaida wa kotu

Wani mutum, Ismail Yussuff, ya shaida wa wata kotu ta musamman da ke Ile Tuntun a yankin Oja Oba, a garin Ibadan, babban jihar Oyo, cewar ya gaji da matar sa, Khadijat Yuusfuf, tare da rokon kotun ta raba auren su.

"Mai girma, mai shari'a, mata ta na da mugayen halaye da yawa. Makaryaciya ce, barauniya, ga son fada kamar dage. Maci amana ce. Na kawo ta kara wannan kotu ne saboda tayi aure da wani mutum alhalin muna zaune tare a matsayin mata da miji," a cewar Isamail.

A takardar sa ta korafi da ya gabatar a gaban kotu, Ismail ya ce matar sa ta hana shi samun kwanciyar hankali. Ya bayyana wa kotun cewar matar ta sa makarciya ce da ba ta gajiya da fada.

Ismail ya kara da cewa, Khadijat ta kware wajen iya sata da cin amanar aure, tare da sanar da kotun cewar ta yi aure da wani mutum a boye, ba tare da saninsa ba.

Cakwakiya: Mata ta tayi aure alhalin muna tare - Miji ya shaida wa kotu
Cakwakiya: Mata ta tayi aure alhalin muna tare - Miji ya shaida wa kotu
Asali: Depositphotos

Fusataccen mijin ya roki kotu ta raba aurensu, sannan ta bashi damar cigaba da rikon 'ya'ya uku da su ka haifa tare.

Sai dai, Khadijat ta karyata wadanan zarge-zarge da Ismail ya zayyana a gaban kotu tare da bayyana mijin na ta ke gaza ciyar da ita da lakada ma ta duka duk lokacin da ta tambaye shi kudin abinci.

DUBA WANNAN: Kyautar manyan motoci: Sheikh Bala Lau ya kare kan sa

Kazalika, ta sanar da kotun cewar Ismail ba ya ganin kima ko utuncin ta domin har mata ya ke kawo wa cikin gidan su na aure, su kwana tare.

"Yana duka na, yana kawo matan banza ya kwanta da su a kan gadon mu na aure. Mun taba yin fada har aka raba auren mu a wata kotu, kuma bayan hakan ne na auri wani mijin. Amma daga baya an yi mana sulhu, na dawo gidansa," a kalaman Khadijat

Alkalin kotun, Cif Olasunkanmi Agbaje, ya daga sauraron karar, tare da umartar ma'auratan su dawo kotun tare da iyaye ko wakilansu da kuma yaran da su ka haifa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel