Naji haushi da aka kama ni kafin na saci komai, inji wani barawo

Naji haushi da aka kama ni kafin na saci komai, inji wani barawo

Wani Akeem Azeez da aka gurfanar da kotu a ranar Juma'a ya bawa mutanen da ke kotun mamaki yayin da ya ce ya yi nadamar kama shi da akayi kafin ya shiga gidan da zai yi satan.

An gurfanar da matashin dan shekaru 20 ne tare da wani Omisakin Sunday mai shekaru 24 bisa zarginsa da yunkurin yin kutse gidan wani domin yin sata.

An gurfanar da matasan biyu ne gaban alkali Olusegun Ayilara na kotun Majistare da ke garin Osogbo bisa tuhumar sata, kutse da balle kofar gida ba tare da izinin ba.

Wadanda ake tuhumar su biyu duk sun amsa laifinsu.

Nayi bakin cikin kama ni da akayi kafin in aikata sata - Wanda ake zargi
Nayi bakin cikin kama ni da akayi kafin in aikata sata - Wanda ake zargi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zabe: Dalilin da yasa Amurka ke goyon baya na - Atiku

A baya, dan sandan mai gabatar da kara, Rasak Olayiwola ya shaidawa kotu cewa a ranar 17 ga watan Janairun 2019 ne misalin karfe 11.30 na safe matasan biyu suka hada baki suka aikata laifin a gidan wani Alhaji Rasaq Okunade da ke lamba 23 Ayegun Street, Iludun a garin Osogbo.

Dan sandan ya ce an cafke su kafin suyi nasarar kutsawa cikin gidan.

A yayin yanke hukunci, alkalin ya bukaci a cigaba da tsare su a hannun 'yan sanda kuma ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 13 ga watan Fabrairun 2013 domin a gabatar da hujoji.

A yayin da alkalin ya bayar da umurnin a tsare su, daya daga cikin wanda ake zargin Azeez ya ce ya yi nadamar rashin nasarar aikata satar da su kayi domin za a hukunta shi duk da cewa bai yi nasarar aikata satar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel