Arsenal, Man Utd, Real, PSG sun yi nasara, Chelsea ta sha kashi a makon yau
Wannan karo mun leka bangaren wasanni inda mu ka kawo maku abarin wasannin kwallon kafa na wannan makon inda ake cigaba da fafatawa a gasan kasahen Ingila, da Faransa da Italiya da Sifen da sauran su.
Mun kawo yadda aka kare a manyan wasannin da aka buga jiya:
1. Arsenal v Chelsea
Arsenal ta lallasa kungiyar Chelsea a wasan da aka kara jiya da ci 2-0. Wannan abu ya sa kocin kungiyar watau Maurizio Sarri ya fusata ganin yadda ya sha kashi a babban wasan na Landan.
2. Liverpool v Crystal Palace
Wasan Liverpool da Crystal Palace yayi zafi inda aka tashi 4-3. Dan wasa Mohammed Salah ya ci kwalla 2 a wasan. Yanzu dai Liverpool tana cigaba da yin zaman dirshen a gasar Firimiya.
KU KARANTA: Manyan ‘Yan kwallo 5 da su ka fi kowa samun kudi a fadin Duniya
3. Manchester United v Brighton
Manchester United da sabon kocin ta watau Ole Gunner Solskjaer ta sake samun nasara a wasan makon nan. United ta yi nasara a wasanni 7 cikin 7 da ta buga bayan korar Jose Mourinho.
4. Real Madrid v Sevilla
Idan mu ka koma kasar Sifen kuma za mu ji cewa Real Madrid ta samu galaba a kan Kungiyar Sevilla da ci 2 da nema. Real ta samu wannan asara ne ta hannun ‘yan wasannin ta na tsakiya.
5. PSG v Guingamp
A kasar Faransa kuwa PSG tayi wa kungiyar Guingamp dukan babban bargo inda ta dirka mata ci har 9 da nema. Kyalian Mbappe da Edison Cavani su ka zura kwallaye 3 inda Neymar ya ci 2.
Irin su Man City sun yi nasara a wasan da su ka buga yau da ci 3-0. A kasar Italiya kuwa, Juventus za tayi wasa ne ranar Litinin. A Jamus kuma Dortmund wanda ke jan ragamar tebur ta ci wasan ta, haka kuma Bayern Munich.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng