Ana kishin-kishin din El-Rufai ya ba Sheikh Bala Lau sababbin motoci

Ana kishin-kishin din El-Rufai ya ba Sheikh Bala Lau sababbin motoci

Mun fara jin jita-jita yana cewa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya rabawa shugaban kungiyar Izala na kasa watau Sheikh Abdullahi Bala Lau wasu sababbin motoci kwanan nan.

Ana kishin-kishin din El-Rufai ya ba Sheikh Bala Lau sababbin motoci
An aikawa Shugaban Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatus Sunnah motoci
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne kusan kwana biyu bayan shugaban kungiyar JIBWIS watau Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatus Sunnah din na kasa ya fito ya bayyanawa Duniya cewa Mabiyan kungiyar sa za su marawa Buhari baya ne a 2019.

Sahara Reporters ta rahoto mana cewa an kai wa babban Malamin motocin ne har gidan sa da ke kan lamba na 23 a cikin lungun N'Djamena Crescent a Unguwar Wuse 11. Gidan malamin yana kallon otel dinnan na Gombe Jewel.

KU KARANTA: Kan Malaman Arewa ya rabu a game da zaben Buhari da Atiku

Shehin Malamin dai ya tabbatar da cewa ‘Yan Izala za su zabi Buhari ne a 2019, wanda bayan nan aka ji cewa an aika masa da mota kirar jeep ta samfarin Toyota Land Cruiser Jeep wanda ake yayi, a gidan sa da ke birnin tarayya Abuja.

Bayan nan kuma SaharaReporters tace ta hangi wata sabuwar mota fil kirar Space Wagon Sienna wanda ta fito a shekarar 2017 a cikin gidan Malamin. Sai dai har yanzu ba mu da tabbacin cewa gwamnan Kaduna ne ya aikawa Shehin.

Kwanan nan ne dai Sakataren kungiyar ta Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatus Sunnah na kasa watau Sheikh Kabir Haruna Gombe ya koka da yadda jama’a ke zargin su da yi wa Buhari kamfe a ko yaushe su kace a zabi mutanen kwarai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel