An rushe gwamnatin Burkina Faso mai makwabtaka da Sokoto a Sahara

An rushe gwamnatin Burkina Faso mai makwabtaka da Sokoto a Sahara

- Firayim ministan Burkina Faso ya aje aiki

- Hakan ya biyo bayan bukatar yan kasar sakamakon barazanar tsaro da kasar take fuskanta

- Shugaban kasar ya amince da aje aikin tare da mika godiyar shi ga firayim ministan da sauran ministocin

An rushe gwamnatin Burkina Faso mai makwabtaka da Sokoto a Sahara
An rushe gwamnatin Burkina Faso mai makwabtaka da Sokoto a Sahara
Asali: UGC

Gwamnatin Burkina Faso da firayim minista Paul Kaba Theiba sun aje aiki a ranar juma'a, kamar yanda takardar sa shugaban kasar ya saki tace.

Babu bayani akan aje aikin duk da wata majiya ta sanar da AFP, shugaban kasa Roch Marc Christian Kabore na son shakar iska tare da watayawa a shugabancin kasar Afirka ta yamman, wacce ke yaki da farmakin yan jihadi da masu sace mutane.

Edith Blais yar kasar Canada, mai shekaru 34 da Luca Tacchetto dan shekaru 30 dan kasar Italia sun bace tun tsakiyar watan Disamba, kuma da yammacin ranar laraba an ga gawar wani dan kasar Canada masani a harkar ma'adanai a wani gurin hakar zinare w arewa maso yamma.

"Da rana ne firayim minista Paul Kaba Thieba ya kai takardun aje aiki tare da barin gwamnatin,"

"Shugaban kasar Faso ya amince da aje aikin tare da nuna godiyar shi ga firayim minista Paul Kaba Thieba ga duk ministocin akan maida hankali da sukayi a aiyukan su," takardar ta kara da.

Shugaban kasa Kabore ya zabi masanin tattalin arziki Thieba a matsayin firayim minista a watan Janairu 2016. Amma kuma a watannin nan yan siyasar adawa suna ta magana akan ya aje aiki shi da ministocin tsaro.

GA WANNAN: Har sabon shugaban sufeton 'yansanda ya fara samun karbuwa a duniya, gabanin zabe

Burkina Faso na fama da kashe kashe sakamakon ta'addancin yan jihadi.

Yankin ya hargitse ne da fadace fadacen masu tsaurarawa akan addini bayan da rikicin ya shanye Libya a 2011.

Ta'addancin masu ci da addinin musulunci ya fara a arewacin Mali, Boko Haram kuma a arewacin Najeriya.

Samamen masu jihadin ya fara a arewacin Burkina Faso a 2015 kafin yaduwar shi zuwa gabashin kasar kusa da iyakar Togo da jamhuriyar Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel