Bauchi: 'Yan takarar gwamna da wasu jiga-jigan 'yan siyasa a jihar na shirin kayar da gwamnatin APC

Bauchi: 'Yan takarar gwamna da wasu jiga-jigan 'yan siyasa a jihar na shirin kayar da gwamnatin APC

Wata kwakwarar majiya ta bayana cewa 'yan takarar gwamna da wasu masu ruwa da tsaki daga jihar Bauchi sunyi taro a Abuja domin tsayar da dan takara guda da zai kayar da gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC da ke kan karagar mulki yanzu inji Daily Trust.

Dan takarar gwamna na New Nigerian Peoples Paty (NNNP) ya tabbatar wa majiyar Legit.ng cewa anyi taron a Abuja a hirar wayar tarho da su kayi.

"Eh, munyi taro a Abuja inda ake nemi mu tsayar da mutum guda amma dukanmu mun ce bamu amince da hakan ba domin lokaci ya kure, saboda haka kowa zai cigaba da kamfen dinsa," inji shi.

Bauchi: 'Yan takarar gwamna da wasu jiga-jigan 'yan siyasa a jihar na shirin kayar da gwamnatin APC
Bauchi: 'Yan takarar gwamna da wasu jiga-jigan 'yan siyasa a jihar na shirin kayar da gwamnatin APC
Asali: UGC

Shugaban Green Party of Nigeria reshen jihar Bauchi, Alhaji Sani Burra shima ya tabbatar da cewa anyi taro a Abuja inda aka tattauna batun tsayar da dan takara guda.

DUBA WANNAN: Sultan ya yi gargadi a kan hasashen zaben shugaban kasa da limaman coci ke yi

Kazalika, shugaban PRP na jihar Bauchi, Alhaji Shehu Barau Ningi ya tabbatar da cewa dan takarar gwamna na jam'iyyar, Farfesa Mohammed Ali Pate ya halarci taron na Abuja.

Sai dai bai yi bayani a kan abinda aka tattauna ba.

A bangaren sa, sakataren tsare-tsaren na APC a jihar, Lawan Gyan-Gyan ya ce mahallarta taron kawai suna bata lokacin su ne.

"Sun dade suna wannan kule-kullen domin hambarar da Gwamna Abubakar amma ba su cin nasara. Tarin 'yan siyasa ne kawai masu kwadayin mulki da son kai.

"Ina tabbatar maka babu wani cikinsu da zai amince ya hakura ya bar ma wani. Mutanen Bauchi ne suka zabi Gwamna Abubakar a 2015 inda ya samu kuri'u mafi yawa a tarihin jihar," inji shi.

A cewar INEC, jam'iyyun siyasa 28 ne suka fitar yan takarar gwamna a jihar ta Bauchi. Sai dai ba san adadin waɗanda suka hallarci taron ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel