An fara biyan yan Najeriya makudan kudi domin su fita daga wata kasar Turai
Gwamnatin kasar Czech Republic ta shirya wani sabon tsari da za ta biya bakin haure makudan kudade da nufin su fita daga kasarta ba tare da sun sake komawa ba, kamar yadda wata jaridar kasar, Remix, ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya da yan Najeriya, gwamnatin kasar Czech Republic ta nemi duk wasu bakin haure da suka fito daga kasashen Iraqi, Mongolia, Rasha da Vietnam dasu rungumi wanna tsari, kuma su yi amfani da wannan dama domin samun kudin fita daga kasar cikin ruwan sanyi.
KU KARANTA; An karrama mutane 6 da suka nuna halaye irin na Sir Ahmadu Bello Sardauna a Kaduna
Ita dai kasar Czech tana cikin yankin nahiyar Turai ne, kuma karamar kasa mai karancin yawan jama’a, don haka take neman duk wasu bakin hauren da bata yi musu maraba ba dasu tattara inasu inasu su fice.
Sharadin samun wannan kudi shine bakin ba zasu sake komawa kasar ba, amma zasu iya shiga wata kasar ta daban a nahiyar Turai, ga duk wanda ya amince da wannan sharadi, zai samu Czech Koruna 40,000 zuwa Czech Koruna 100, kimanin N647,200 zuwa N1,618,000.
Ministan harkokin cikin gida na kasar, Jan Hamacek ya bayyana cewa wannan kudi zai taimaka ma bakin haure wajen biyan kudin jirgi, wajen zama, sayan kaya daki, kiwon dabbobi da kuma sauran abin da zasu yi hidima dasu.
Ministan yace gwamnatin kasar Czech Republic ta ware kimanin kudi pan miliyan 2.3, wanda kaso 75 daga cikin kudin zasu fito ne ta hannun asusun tallafa ma yan gudun hijira na kungiyar kasashen nahiyar Turai.
Sai dai a yanzu haka kasashen Turai da dama sun fara shirya kwatankwacin wannan shiri domin su rage adadin bakin hauren dake cikin kasashensu, wannan tsari ya fara karbuwa a kasashen ne saboda tsadar dawainiya da fursunonin gidajen yari, don haka sun gaji da kai bakin haure kurkuku suna musu hidima.
Haka zalika sun bayyana cewa idan suka cigaba da kama bakin haure suna mayar dasu kasashensu zasu cigaba da asarar makudan kudade, amma da wannan tsarin zasu kashe kudi kadan, kuma su samu biyan bukata.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng