Dalilan da suka sanya na shekara 13 ban shiga America ba - Atiku

Dalilan da suka sanya na shekara 13 ban shiga America ba - Atiku

- Dalilan da suka hana Atiku Abubakar shiga kasar Amurka

- A ranar alhamis ne Atiku ya sauka a birnin Washington DC

- Ana zargin shi ne da laifin karbar cin hanci daga Siemens

Dalilan da suka sanya na shekara 13 ban shiga America ba - Atiku
Dalilan da suka sanya na shekara 13 ban shiga America ba - Atiku
Asali: Twitter

A fiye da shekaru 13, Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma yanzu dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar PDP ya guji Amurka.

Akwai lokacin da US din ta hana shi Visa. Amma a ranar alhamis sai gashi ya sauka a birnin Washington DC don tattaunawa da wasu jami'an Amurka akan yakin neman zaben shi a Najeriya.

Ziyarar wacce tsohon mai gidan shi Olusegun Obasanjo da wasu magoya bayan shi suka assasa, ya jawo tambayoyin dalilin da yasa Atiku ya guji zuwa Amurka tuntuni.

Abinda ya faru a shekaru 9 da suka wuce, akwai wani kwamitin majalisar US da ta bada rahoto akan almundahanar kudi akan shi wanda ya hada da karbar cin hanci daga Siemens. Kwamitin da sanata Carl Levin ya jagoranta ya bayyana illolin rashawa a cigaban gwamnati, dokokin damokaradiyya da dokokin shugabanci.

"An san ta lalata kasuwa, korar hannayen jari, zurfafa talauci da kawo yawan laifuka. Akwai alaka mai karfi tsakanin rashawa, rusassar kasa da ta'addanci. Rashawa ta cigaba da zama babbar matsala. Bankin duniya ya kintata dala tiriliyan ta rashawa 1 ce ke shiga cikin cinikayya a duk shekara a fadin duniya," kamar yanda kwamitin ya bayyana a rahoton shi.

GA WANNAN: An sake waiwayar dumbin dukiyar da Alex Badeh ya bari, sai dai an daga kafa har ayi jana'izarsa

Abubakar ba shi kadai bane dan siyasar wata kasa da kwamitin ya fallasa ba. Akwai Teodoro Nguema Obiang Mangue, marigayi shugaban kasar Gabon Omar Bongo da wasu asusun bankuna 3 na wasu yan siyasar da ba a kasar Amurka suke ba wanda aka samu da laifin safarar makamai, wani jami'in gwamnati da wani karamin banki mai zaman kanshi.

Kwamitin ya mika rahoton ne a 4 ga watan Fabrairu 2010, shekaru uku bayan da Abubakar ya sauka dag kujerar shi ta mataimakin shugaban kasa.

Rahoton ya bayyana taka dokokin US da Abubakar tare da matar shi ta hudu, Jennifer Doughlas suka yi. Ya kuma bayyana cin hancin Siemens da ya shiga daya daga cikin asusun bankin shi. Wannan shine tushen abinda yasa aka hana Abubakar shiga kasar Amurka.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel