Gwamnan Sokoto Tambuwal yana neman Jama’a su marawa PDP baya
- Gwamna Aminu Tambuwal ya nemi jama’an Sokoto su zabe sa a 2019
- Mai Girma Gwamnan yayi alkawarin yin manyan ayyuka idan ya zarce
- Tambuwal yana neman tazarce a PDP ne bayan ya sauya-sheka kwanaki
Labari ya iso gare mu daga jaridar nan ta Daily Trust ta kasar nan cewa gwaman Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya na cigaba da kokarin ganin mutanen jihar sa sun kuma zaben sa a karo na biyu a zaben da za ayi.
Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, yayi kira ga mutanen jihar Sokoto su zabe sa a 2019 inda yayi alkawarin cewa za a ga manyan aikace-aikace idan har ya zarce a kan mulki. Gwamnan yayi wannan kira ne wajen wani kamfe.
KU KARANTA: Gwamnan Kebbi ya sha alwashin ganin Buhari ya samu tarin kuri’a
Kamar yadda mu ka samu labari, mai girma gwamnan na Sokoto ya shiga karamar hukumar Silame a cikin makon nan. A wannan gari ne Tambuwal ya nemi jama’a su zabi PDP a kowane mataki domin a shawo kan matsalolin kasar.
Gwamnan ya bayyana cewa za a ga karin ayyuka muddin ya samu zarcewa a kan kujerar da yake kai. Aminu Tambuwal yayi wannan alkawari ne a lokacin da jirgin yakin neman zaben na sa ya shiga cikin karamar hukumar Silame.
Darektan yakin neman zaben PDP a Sokoto, Mukhtari Maigona ya halarci wannan taro inda yayi kira ga jama’a su zabi PDP a dalilin talauci da yunwa da yace gwamnatin APC ta jefa mutanen a cikin shekaru 3 da rabi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng