Ko me nayi, Kiristocin Kaduna ba za su zabe ni ba – Inji El-Rufai

Ko me nayi, Kiristocin Kaduna ba za su zabe ni ba – Inji El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna State ya bayyana cewa ba shi da rabo wajen kiristocin jihar a zaben 2019. Gwamnan yace ko me zai faru ya cire rai cewa kiristocin Kaduna za su zabe sa bana.

Ko me nayi, Kiristocin Kaduna ba za su zabe ni ba – Inji El-Rufai
El-Rufai yace ya ci zabe ya gama duk da Abokiyar takarasa Musulma ce
Asali: Twitter

Mai girma Gwamnan yake cewa ko da zai samu Fafaroma a matsayin Abokin takarar sa a zaben bana, kusan kashi 67% na kiristocin da ke jihar Kaduna ba za su kada masa kuri’a ba, don hake ne yace ya dauko Musulma ta taya sa takara.

El-Rufai yayi magana a game da matakin da ya dauka na tsaida ‘Yar uwar sa Musulma domin ta zama mataimakiyar sa idan ya ci zabe. Gwamnan yayi wannan jawabi ne a Ranar Alhamis dinnan a gidan Talabijin na Channelsa TV.

Gwamnan ya nuna cewa daukar Kirista a matsayin Abokin takarar sa a 2019 ba zai canza komai ba a jihar Kaduna, inda ya nuna cewa akwai bukatar a rika bada fifiko game da cancanta da nagarta a maimakon addini ko kuma kabila.

KU KARANTA: Lokaci APC ta ke jira a sanar cewa ta ci zabe - Mataimakin El-Rufai

Malam Nasir El-Rufai yake cewa sai da mutanen kudancin Kaduna su ka fara yi wa mataimakin sa mai shirin barin gado watau Yusuf Bala Bantex, kallon saniyar ware saboda kurum yana cikin tafiyar APC duk da cewa kuma yana kirista.

Gwamnan ya tunawa jama’a tarihin rikicin da aka rika yi a Kaduna tun 1992 wanda tsaida kirista a matsayin mataimakin gwamna bai canza komai ba. A zaben bana ma Gwamnan yana ganin ko me yayi ba zai canza ra’ayin jama’an ba.

A karshe gwamna yake cewa PDP ba ta taba lashe zabe a Kaduna ba, sai dai kurum tayi magudi kusan duk zabe. Malam Nasir El-Rufai ya nuna cewa yana da tabbacin lashe zaben gwamna da za ayi kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel