Sultan ya yi gargadi a kan hasashen zaben shugaban kasa da limaman coci ke yi

Sultan ya yi gargadi a kan hasashen zaben shugaban kasa da limaman coci ke yi

- Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar ya yi kira ga shugabanin addini suyi takatsantsan kan wajen tallata ra'ayoyinsu a kan zaben 2019

- Sarkin Musulmi kuma Shugaban Kwamitin Koli ta addinin Musulunci ya gargadi 'yan siyasa su guji tayar da zaune tsaye

- Sa'ad Abubakar ya gargadi shugabanin addini su kiyaye irin abubuwan da suke fadawa mabiyansu a coci da masallatai

Sultan na Sokoto kuma Shugaban kwamitin koli ta harkokin addinin musulunci, Muhammadu Sa'ad Abubakar ya yi kira ga shugabanin addinai suyi takatsantsan wurin tallata ra'ayoyinsu gabanin babban zaben 2019.

Sultan ya yi a kan hasashen zaben shugaban kasa da limaman coci ke yi
Sultan ya yi a kan hasashen zaben shugaban kasa da limaman coci ke yi
Asali: Facebook

Sarkin Musulmin ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wasu malaman addini ke hasashen 'yan takarar da za su lashe zaben inda ya yi gargadin cewa hakan na iya tayar da hankulan al'umma kafin zaben kamar yadda Guardian ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Taron jin ra'ayi: Dalilin da yasa ban ce komai ba game da zargin rashawar da ake yiwa Ganduje - Buhari

Legi.ng ta gano cewa ya yi wannan jawabin ne a garin Abuja wurin taron Tattaunawa tsakanin mabanbantan addinina (IDFP) da akayi a ranar Laraba 16 ga watan Janairun 2019.

Ya ce: "A matsayin mu na shugabanin addini, ya zama dole muyi takatsantsan a kan abubuwan da muke fadawa mabiyan addinan mu a masallatai da coci saboda mun san cewa wata rana zamu tashi gaban Allah mu bayar da sheda. Kar mu amince 'yan siyasa suyi amfani da mu. Idan kana goyon bayan wata jam'iyya ko dan siyasa, ko bar ma zuciyarka ka jefa masa kuri'an ka.

"Shugabanin addini su rika koyar da mabiya addinai kaunar juna da tsoron Allah a duk abinda za suyi. Shugaba Buhari ya yi alkawarin gudanar da zabe mai tsafta. Amma shin hukumomin tsaro da 'yan siyasa sun shirya?"

A jawabinsa, Shugaban kungiyar Kirista ta Najeriya (CAN), Dr Samson Ayokunle ya yi kira ga hukumomin tsaro su guji nuna fifiko ga kowanne dan siyasa a yayin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel