Rundunar Yansandan Najeriya ta kama wani mutum da laifin kokarin kashe kansa

Rundunar Yansandan Najeriya ta kama wani mutum da laifin kokarin kashe kansa

Rundunar Yansandan Najeriya ta kama wani mutumi da bata bayyana sunansa ba da laifin kokarin kashe kansa a ranar Talata 15 ga watan Janairu a jahar Legas, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansandan sun dakile yunkurin mutumin ne a lokacin da yayi kokari afkawa cikin tafkin Legas daga saman Third Mainland, tafkin da yayi kaurin suna wajen cin rayukan mutane da dama.

KU KARANTA: Buhari da Osinbajo zasu halarci taron sauraron ra’ayin yan Najeriya da zai gudana a Abuja

Rundunar Yansandan Najeriya ta kama wani mutum da laifin kokarin kashe kansa
Mutum da yayi kokarin kashe kansa
Asali: UGC

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mutumin ya fake ne da daukan wani abu daga saman gadan, yayin da yake tura kansa a tsakanin karafan gadar da nufin kokarin tunjumawa cikin tafkin ba tare da jama’a sun Ankara ba.

Sai dai Allah Yasa akwai wasu jajirtattun jami’an Yansanda dake kan gadan, wanda sune suka hangi mutumin yayin da yake kokarin halaka kansa da kansa, inda suka yi wuf suka kamashi, tare da daukeshi daga kan gadar gaba daya, suka tafi da shi ofishin Yansanda dake Adekunle don gudanar da bincike.

Shima wani mutumi da lamarin ya faru a gabansa, Salami Ogundele yace ya ga mutumin akan gadar yayin da yake tuka motarsa, amma bai fahimci menene manufar mutumin ba. “Amma dole na tsaya da motata a lokacin da na hangi Yansanda sun nufo shi da gudu.”

Idan za’a tuna a watan a Yunin shekarar 2018 data gabata ma an samu wata budurwa da ta tunjuma cikin wannan tafki daga saman gadar Mainland, rahotanni sun bayyana cewa matar ta sauka daga motar tasi ne a saman gadar, sa’annan ta afka cikin tekun, ta kashe kanta.

Bugu da kari an taba samun wani babban likita da shi ma ya kashe kansa a cikin wannan teku sanye da kayan aikinsa, inda wasu abokan aikinsa ke ganin hidindimun aiki ne suka yi masa yawa yasa ya kashe kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: