Lemukan karin kuzari sun fi tabar wiwi hatsari - NDLEA

Lemukan karin kuzari sun fi tabar wiwi hatsari - NDLEA

Hukumar hana sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana cewar lemukan karin kuzari dake wartsakar wa a matsayin masu hatsari ga jiki fiye da tabar wiwi.

Shugaban hukumar NDLEA a jihar Adamawa, Yakubu Kibo, ya bayyana hakan yayin gabatar da lakca a wurin wani taro na kwana daya da aka yi a kan illolin kwayoyi a shugabanci da aka yi a Yola.

Kibo ya nuna damuwa bisa kwararowan lemukan karin kuzari ko a-ji-garau cikin jihar Adamawa.

"Hukumar NDLEA a jihar Adamawa ta damu matuka da karuwar da lemukan karin kuzari (energy drinks) ke yi a kaauwanni.

"Da yawa daga cikin irin wadannan lemukan na da matukar illa, wasu sun fi tabar wiwi hatsari ga jiki," a cewar Kibo.

Lemukan karin kuzari sun fi tabar wiwi hatsari - NDLEA
Jami'an NDLEA
Asali: UGC

Kibo ya bukaci jama'a su kauracewa amfani da lemukan karin kuzari domin sune ke jawo yawaitar fadace-fadace da rigingimu a duniya da ma Najeriya.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta sanar da samun nasarar kama wasu mutane biyu da suka garkuwa da wata dattijuwa a karamar hukumar Safana.

DUBA WANNAN: An kama matashin dan fashi da babbar mota na kokarin shiga kasar Nijar

A wani jawabi da ya yi ga manema labarai a hedkwatar 'yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce sun kama 'yan ta'addar biyu ne bayan samun bayanan sirri.

Ya ce masu mutanen sun amsa laifinsu, kuma matar da suka yi garkuwa da ita ta tabbatar da cewar sune suka sace ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel