Ci-da-addini: EFCC ta yi ram da wani malamin addini dake damfarar mabiyan sa

Ci-da-addini: EFCC ta yi ram da wani malamin addini dake damfarar mabiyan sa

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta ce ta cafke wani malamin addinin Kirista mai suna Giniko Obi dake garin Benin jihar Edo bisa zargin damfara.

Shi dai malamin addinin kamar yadda muka samu yana damfarar mabiyan sa ne a garin Agbor, jihar Delta da wasu garuruwan kuma irin Bayelsa, Onisha, Legas, Fatakwal da Abuja ta hanyar karbar masu makudan kudade.

Ci-da-addini: EFCC ta yi ram da wani malamin addini dake damfarar mabiyan sa

Ci-da-addini: EFCC ta yi ram da wani malamin addini dake damfarar mabiyan sa
Source: UGC

KU KARANTA: Kungiyar Izala ba ta siyasa bace - Gumi

Wannan dai na kunshe ne a cikin sanarwar da jami'in hulda da jama'a na EFCC din Mista Tonu Orilade ya fitar a garin Abuja ranar Litinin din da ta gabata.

Amma da yake bayar da bahasi, Bishop Obi ya ce tsantsar tausayi ne da kuma son taimakon al'umma dake cikin matsanancin talauci ya sa shi cikin halin da ya tsinci kan sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel