Tashin hankali: 'Yan bindiga sun hallaka mutane 26 a Sokoto

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun hallaka mutane 26 a Sokoto

'Yan bindiga sun kashe wani jariri mai shekara daya da ragowar wasu mutane 25 a masarautar Gandhi dake karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar an kai harin ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a kauyukan Warwana, Tabkin Kwasa da Dutsi.

Jaridar ta ce 'yan bindigar sun kashe maza fiye 20 da mata 4.

Wasu da dama daga cikin mazauna kauyukan da suka bar gidajensu, an dauke su zuwa sansanin 'yan gudun hijira dake garin Gandhi, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Wasu shaidar gani da ido sun shaidawa Daily Trust cewar 'yan bindigar sun kai hari kauyukan a kan babura fiye 25.

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun hallaka mutane 26 a Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto; Aminu Tambuwal
Asali: Facebook

Wata majiyar ta ce 'yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi.

Da yake tabbatar da kai harin, kwamishinan 'yan sandan jihar Sokoto, Murtala Mani, ya bayyana cewar an tura karin jami'an 'yan sanda da sojoji zuwa yankin.

Da yake jajantawa hakimin masarautar Gandhi, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Alla-wadai da kai harin.

DUBA WANNAN: An kama masu garkuwa da mutane da fashi da makami Katsina

Kazalika, gwamnan ya soke kaddamar da kamfen dinsa a karamar hukumar Goronyo domin nuna alhini bisa kai harin.

Tambuwal ce gwamnatin jihar zata bawa mazauna sansanin gudun hijira gudunmawar da suke bukata.

Wannnan shine karo na biyu da 'yan bindiga suka kai hari masarautar Gandhi. Sun kai harin farko tare da kashe mutane 30 a watan Yuli na shekarar 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel