Da duminsa: Adamu Lafiya ya zama sabon shugaban rundunar 'yan sanda

Da duminsa: Adamu Lafiya ya zama sabon shugaban rundunar 'yan sanda

Domin gujewa canja shawara a kurarren lokaci, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince wa Abubakar Adamu Mohammed ya zama sabon shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa, kamar yadda jaridar Premium Times ta ce majiyar ta a fadar shugaban kasa ta tabbatar mata.

A yammacin yau, Litinin, ne shugaban rundunar 'yan sanda mai barin gado, Ibrahim Idris, ya ziyarci shugaba Buhari, ziyarar da majiyar 'yan sanda ta ce ta zama al'ada ga duk shugaban rundunar da zai bar aiki.

"Muna da sabon shugaban rundunar 'yan sanda," wani babban jami'in dan sanda ya shaidawa Premium Times a daren yau. "Tuni Ibrahim Idris ya koma gida, ya kwashe kayansa daga gidan gwamnati, yanzu muna jiran kawai ya mika mulki ne," jami'in ya tabbatar.

Kazalika wata majiya a fadar shugaban kasa ta tabbatar wa da jaridar amincewar shugaba Buhari na mika wa Mohammed rundunar 'yan sanda.

Da duminsa: Adamu Lafiya ya zama sabon shugaban rundunar 'yan sanda
Buhari da tsohon shugaban rundunar 'yan sanda, Ibrahim Idris
Asali: UGC

Kafin amincewa da sunansa a matsayin sabon shugaban rundunar 'yan sanda, Mohammed, dan asalin jihar Nasarawa, ya kasance mataimaki ga Sifeton rundunar 'yan sanda. Abokansa na aiki na kiransa da Adamu Lafiya, domin alakanta shi da mahaifar sa, wato babban birnin jihar Nasarawa.

An haifi Mista Mohammed a ranar 9 Nuwamba na shekarar 1961. Ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1986 da takardar kammala karatun digiri a Geography.

DUBA WANNAN: Wata babbar kotu ta hana gurfanar da alkalai, ta jero dalilai

Ya rike mukamin darektan aiyukan jami'an 'yan sanda a kasashen ketare, tsohon kwamishinan 'yan sanda ne a jihar Enugu kafin daga bisani ya zama mataimakin shugaban rundunar 'yan sanda mai kula da rukuni na 5.

Nadin Mohammed a matsayin IGP zai tilasta manyan mataimakan shugaban rundunar 'yan sanda da yawa yin murabus kamar yadda ta faru bayan shugaba Buhari ya nada Idris a matsayin IGP a shekarar 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel