Kwankwasiyya: Kotu tayi watsi da karar neman hana Abba takara a Kano
- Kotu tayi watsi da karar da dan takarar gwamna a PDP, Jaafar Sani-Bello ya shigar ne neman a hana Abba Yusuf takara
- Kotun tayi watsi da karar nasa ne saboda ba a shigar da karar cikin wa'addin kwanaki 14 bayan zabe da doka ya tanada ba ga masu karar zabe
- Jaafar Sani-Bello ya ce zaiyi shawara da na kusa dashi domin sannin matakin da zai dauka amma ya ce ba zai fice daga PDP ba
A ranar Litinin ne wata babban kotu da ke Kano tayi watsi da karar da wani dan takarar gwamna a PDP, Jaafar Sani-Bello ya shigar ne neman haramtawa dan takarar jam'iyyar PDP na jihar, Abba Yusuf takara a zaben da ke tafe.
Idan ba a manta ba a ranar 2 ga watan Oktoban 2018 ne, Abba Yusuf, surukin tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP inda ya samu kuri'u 2,421 inda ya kayar da abokin hammayarsa Sani-Bello wanda ya samu kuri'u 1,258.
Sai dai Sani-Bello bai gamsu da sakamakon zaben ba hakan yasa ya garzaya babban kotu yana bukatar a soke takarar Abba Yusuf saboda ya sabawa sashi na 8 (8) na kundin tsarin jam'iyyar.
DUBA WANNAN: 2019: Ku zabi Buhari, kungiyar Izala ta umurci 'ya'yanta
Sashin ya tanada cewa duk wani da ya fita daga jam'iyyar kuma yana son dawowa sai ya rubuta wasika ga sakataren gunduma na jam'iyya ya sanar dashi niyyarsa na dawowa jam'iyyar wadda a cewarsa Sani-Bello abokin hammayarsa bai aikata hakan ba.
Sai dai a yayin da ya ke yanke hukunci, Alkalin Kotun, Ahmad Badamasi ya ce ba a shigar da karar ba cikin wa'addin kwanaki 14 bayan zaben cikin gidan kamar yadda sashi na 285(9) na kudin tsarin mulkin kasa na 1999 ya tanadar.
A cewarsa, duk wani korafi na zabe ana shigar da shi ne cikin wa'addin kwanaki 14 bayan zaben kamar yadda doka ta tanadar.
"Kamar yadda sashi na 285(9) na kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ce, duk wani korafi na zabe ana shigar da shi ne cikin kwanaki 14 bayan zaben.
"An gudanar da zaben cikin gidan ne na PDP a rannakun 1 da 2 ga watan Oktoba inda mai shigar da karar, Jaafar Sani-Bello ya zo na biyu da kuri'u 1,258.
"Mai kara ya shigar da kararsa ne a ranar 16 ga watan Oktoba. A tunaninsa ya cika ka'idar da ake bukata na kwanaki 14 amma idanun kotu bai cika ka'idar ba domin ya wuce kwanaki 14 kafin shigar da karar," inji Badamasi.
A jawabin da ya yi bayan yanke hukuncin, Sani-Bello ya ce zai tuntubi abokan aikinsa domin ya san mataki na gaba da za su dauka. Ya kuma ce zai cigaba da kasancewa dan PDP kuma zai bayar da gudunmawarsa domin ganin jam'iyyar tayi nasara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng