Kungiyar Izala ta bayyana sunan wanda take goyon baya a zaben shugaban kasa na 2019

Kungiyar Izala ta bayyana sunan wanda take goyon baya a zaben shugaban kasa na 2019

A yayin da babban zaben shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, jama’a da ma kungiyoyin siyasa daban daban da dama na bayyana ra’ayinsu game da gwanin da suke so, wanda shi suke tunanin zai kaisu ga tudun mun tsira, su ma kungiyoyin addinai ba’a barsu a baya ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito anan ma shahararriyar kungiyar nan ta addinin Musulunci dake da dimbin mabiya a kasashen Najeriya, Kamaru, Nijar da Chadi, watau kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah ce ta bayyana nata gwanin.

KU KARANTA: Da dumin sa: Hukumar EFCC tayi karin haske game da labarin maganar tsige Magu

Kungiyar Izala ta bayyana sunan wanda take goyon baya a zaben shugaban kasa na 2019

Bala Lau da Buhari
Source: Twitter

Kungiyar ta sanar da gwanin da take ganin ya fi dacewa da mulkin Najeriya kuma ya yafi dacewa da jama’a su zaba a zaben shekarar 2019 ne ta bakin shugaban majalisar malamai ta kungiyar, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo, inda yace Muhammadu Buhari suke so.

Assheikh Jalingo ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a wata babbar Masallaci dake garin Yola ta jahar Adamawa a ranar Juma’ar data gabata, 11 ga watan Janairun 2019, inda yayi tunatarwa akan muhimmancin zaben shugaban nagari da kuma muhimmancin shugabanci nagari.

Shehin Malamin ya gabatar da hudubar ce a ranar da shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau ke aurar da yayansa mata guda biyu a wannan Masallaci, haka zaika shima na’ibinsa ya aurar da diya mace a bayan sallar juma’ar.

Babban sakataren kungiyar Izala, Sheikh Kabir Gombe ne ya jagoranci daurin auren yayan, inda Bala Lau ya aurar da yayansa mata biyu akan sadaki naira dubu hamsin hamsin, auran daya samu halartar manyan baki daga cikinsu akwai gwamnonin jihohin Zamfara da Adamawa, Abdul Aziz Yari da Bindow Jibrilla.

Sauran da suka halarci auren sun hada da babban sakataren fadar shugaban kasa, Jalal Arabi, babban hadimin shugaban kasa ta bangaren watsa labaru, Malam Garba Shehu, da kuma sauran manyan Malamai.

A wani labarin kuma, Gwamna Abdulaziz Yari ya baiwa shugaban kungiyar Izala, reshen garin Jos, Sheikh Yahaya Jingir, kyautar wata babbar motar alfarma tare da mataimakinsa, Sheikh Yusuf Sambo Rigacikun, duk a makon daya gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel