Saudiyya: Wasu mayun fari sun mamaye garin Makkah, hotuna

Saudiyya: Wasu mayun fari sun mamaye garin Makkah, hotuna

- Wani dandazon fari ya mamaye wurare da dama a birnin Makkah na kasar Saudiyya

- Wani faifan bidiyo da aka yada a dandalin sada zumunta ya nuna yadda farin suka mamaye dakin Ka'aba

- Masu aiki a harami sun tashi tsaye domin tsaftace harabar masallacin bayan zubar farin

Wani lamari mai ban mamaki ya faru a kasar Saudiyya bayan wasu gungun ayarin fari sun mamaye babban masallacin harami dake garin Makkah.

A wani faifan bidiyo da aka yada a dandalin sada zumunta ya nuna yadda farin suka mamaye harabar Ka'aba, musamman a sararin samaniya.

An ga farin na hawa jikin mutane da kuma bangon masallacin harami.

Saudiyya: Wasu mayun fari sun mamaye garin Makkah, hotuna

Wasu mayun fari sun mamaye Harami
Source: Facebook

Saudiyya: Wasu mayun fari sun mamaye garin Makkah, hotuna

Wasu mayun fari sun mamaye harami
Source: Facebook

Saudiyya: Wasu mayun fari sun mamaye garin Makkah, hotuna

Wasu mayun fari sun mamaye harami
Source: Facebook

A wani faifan bidiyo da hukumomin kasar suka nuna a dandalin shafin Tuwita, an ga masu aikin tsaftace masallacin na kokarin share farin bayan fesa masu maganin kashe kwari.

DUBA WANNAN: An yi arangama tsakanin 'yan APC da PDP a Ilorin

Sashen yaren larabci na gidan talabijin din CNN ya kira farin da 'bakaken fari 'yan gudun hijira'.

Jawabin hukumar kasar Saudiyya ya bayyana cewar, "kwararrun jami'ai sun shiga aiki domin kawar da kwarin.

"Akwai ma'aikata 22 dauke da kayan aiki 111 domin yin maganin wadannan kwari cikin gaggawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel