Cikin Hotuna: Kwanaki 3 bayan rasuwar Sarkin Lafia, Marigayi Isa Agwai
A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka gudanar da jana'izar sarkin Lafia, Marigayi Isa Al-Mustapha Agwai I, bisa jagorancin babban Limamin jihar Nasarawa, Mallam Dalhatu Muhammad Dahiru tare da 'yan uwa, makusanta da abokanan arziki.
A ranar Alhamis din makon da ya gabata, Marigayi Isa bayan shafe shekaru 43 bisa karagar mulki ya riga mu gidan gaskiya a wani asibitin koyarwa na kasar Turkiya da ke garin Abuja bayan ya shafa da wata 'yar gajeruwar lafiya.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Marigayi Isa ya rasu ya bar 'ya'ya biyu; Alhaji Musa Isa Mustapha Agwai da kuma Hajiya Hauwa Isa Mustapha Agwai.
KARANTA KUMA: Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a kasar Zimbabwe
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng