Tsohon kwamishinan Jigawa Baba Santali ya koma Jam'iyyar APC

Tsohon kwamishinan Jigawa Baba Santali ya koma Jam'iyyar APC

A cikin karshen makon nan ne mu ka samu labari cewa wani babban ‘Dan PDP a jihar Jigawa ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Hakan na zuwa ne yayin da ake shiryawa babban zaben 2019.

Tsohon kwamishinan Jigawa Baba Santali ya koma Jam'iyyar APC

Wani 'dan siyasa a Jigawa ya ruga Jam’iyyar APC daga PDP
Source: Twitter

Aliyu Baba-Santali, wanda yana cikin manyan na-kusa da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP ne a makon nan. Baba-Santali yana cikin manyan PDP a lokacin gwamnatin Sule Lamido.

Babban ‘dan siyasar ya rike mukamin kwamishinan ayyuka da gidaje ne a lokacin PDP tana mulkin jihar Jigawa. Alhaji Ali Baba-Santali ya sanar da komawar sa APC ne a Garin san a Kazaure a Ranar Juma’ar nan da ta gabata.

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan APC ya fara kuri cewa sun ci zabe sun gama

Daily Nigerian ta rahoto cewa Baba-Santali ya karbi katin zama ‘dan jam’iyyar APC ne a gaban dinbin jama’a masu goyon bayan sa a cikin karamar hukumar Kazaure. Santali yana cikin rikakkun ‘yan siyasa da ake ji da su a yankin.

Daga cikin wadanda su ka bi tsohon kwamishinan zuwa APC akwai tsohon shugaban PDP na Garin Kazaure da kuma mataimakan su. Bayan haka kuma akwai tarin masoya da ‘dan siyasar ya dauke daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

Santali ya taba rike matsayin shugaban karamar hukumar sa ta Kazaure, bayan nan kuma ya taba zama cikin masu ba tsohon gwamnan jihar watau Samini Turaki shawara. Yanzu ‘dan siyasar zai taya APC yakin neman zabe a 2019.

Kwanakin bayan wasu wanda su ka rike mukamin kwamishina a gwamnatin Sule Lamido su ka tsere zuwa APC. Daga cikin su akwai; Auwalu Harbo, Yakubu Ruba, Nasidi Ali, da kuma Fatima Widi-Jalo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel