Labarin Hajiya Aisha Lemu: Shaidar kirki daga bakin danta

Labarin Hajiya Aisha Lemu: Shaidar kirki daga bakin danta

- Dan marigayiya Aisha Lemu na farko yace ba zai manta da halayen ta nagari ba

- Kungiyar NASFAT ta kai ziyarar ta'aziyyar ta a Minna

- An kwatanta ta da musulma ta gari da ba za'a iya samun irin ta ba

Labarin Hajiya Aisha Lemu: Shaidar kirki daga bakin danta

Labarin Hajiya Aisha Lemu: Shaidar kirki daga bakin danta
Source: Facebook

Nuruddeen Lemu, dan fari na marigayiya Aisha Lemu, yace abinda zai fi kewa game da mahaifiyar shi shine yanda ta dauki rayuwa da sauki ko a lokutan kalubale.Nuruddeen Lemu, dan fari na marigayiya Aisha Lemu, yace abinda zai fi kewa game da mahaifiyar shi shine yanda ta dauki rayuwa da sauki ko a lokutan kalubale.

Mista Lemu ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da ofishin dillancin labarai bayan sallar jam'i da kungiyar Nasrul-Lahi-Li Fathi a yayi da suka kai musu ziyara a Minna.

"Mahaifiya ta uwa ce ta gari da Allah ya bamu. Yanda ta dau rayuwa daban ne. Duk yanda kake kallon matsala ita ba haka take kallon ta ba. Ita tunanin ta yanda zamu rayuwa da wannan,ya kuma zamu cigaba. Ita gareta a rayuwa babu wata matsala," inji shi.

Mista Lemu yace iyalan sun san aiyukan ta na lada da kuma yaran da ta dau nauyin karatun su ne bayan rasuwar ta.

"A matsayin mu na iyalan ta, sai bayan da ta rasu ne muka gano yara da mutanen da suka dauke ta uwa kamar mu. Daga nakasassu da kuma wasu ma da bamu san ta dau nauyin su ba saboda muna makaranta bamu san me ke faruwa ba. Abinda muka sani shine, idan mun dawo gida, mahaifiyar mu na kula damu. Toh duk abinda takeyi idan bama nan sai yanzu muke sani," inji shi.

Kamar yanda yace, zai so a dinga tuna mahaifiyar shi a matsayin musulma ta gari.

"Inaso mu dinga tuna ta akan abinda Allah yake so mu tuna ta saboda ta zama wakiliya a doron kasa. Mu tuna ta saboda ta kasance musulma ta gari, tazo daga wata kasa kuma ta koyar damu addini, ta tafi ta bar mana babban abin tunawa."

A wata tattaunawa ta daban, Shugaban NASFAT na kasa, Kamil Bolarinwa yace akwai wuya a samu musulma ta gari kamar Aisha Lemu a ko ina a duniya.

GA WANNAN: Abin tausayi a jihar Anambra, gobara da aka kasa fahimtar yadda tazo, ta kashe yara

"Idan muka gani ko karanta abinda mutane da yawa suka ce, zaka fara tunanin abinda zaka kara. Amma idan ka karanta Qur'ani ko Hadisi kuma ka fahimci musulunci, hanya mafi sauki ta kwatanta mama shine kace bazaka taba samun musulma ta gari fiye da ita a ko ina," inji shi.

Mista Bolarinwa ya jaddada cewa Najeriya ta rasa masaniya wacce da wuya a samu mai cike gurbin ta.

A bangaren shugaban da'awa na NASFAT, Imam Abdulazeez Onike, wanda ya tattauna da ofishin dillancin labarai, ya kwatanta marigayiyar da wacce take iya kokarin ta wajen ganin ta taimaka wa mutane koda zata takura kanta.

Mista Onike yace Aisha Lemu ta canza rayuwar kowanne matashi musulmi a Najeriya.

"Tana cikin masu sadaka da hada shirye shiryen cigaban mutane kuma wadanda suka taba aiki da ita bazasu taba manta ta ba," inji shi.

Ya yabawa marigayiyar akan kirkiro da IET , cewa da sauran musulmai zasu iya koyi da ita wajen kirkiro tsangayoyi na sadaka da aiyukan alheri wadanda zasu bi su ko bayan mutuwa.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa Aisha Lemu, baturiyar marubuciya kuma malamar addinin islama ta rasu a ranar 5 gari watan janairu a Minna, ta bar mijinta Sheikh Ahmed Lemu da yaya biyu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel