Abin tausayi a jihar Anambra, gobara da aka kasa fahimtar yadda tazo, ta kashe yara

Abin tausayi a jihar Anambra, gobara da aka kasa fahimtar yadda tazo, ta kashe yara

- Gobara ta yi sanadin rayukan yara uku a Anambra

- Gobarar da ta lashe kwantena biyu da gida daya har yanzu ba a gano asalin ta ba

- Tuni likitoci suka tabbatar da mutuwar yaran

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Source: Twitter

'Yan sanda a jihar Anambra sun tabbatar da mutuwar yara uku sakamakon gagarumar gobara da aka yi a Obosi, yankin Idemili na jihar a ranar alhamis.

A takardar da jami'in hulda da jama'a na yan sandan jihar SP Haruna Mohammed yasa hannu, yayi bayanin cewa abun ya faru ne wajen karfe 2: 15 na ranar a titin makarantar High tension dake Ugwuagba Obosi.

Yace kwantena biyu wadanda ake saide saide a cikin su da wani gida akan titin suka kama da wuta wanda har yanzu ba a san musababin wutar ba.

"Daya daga cikin masu kwantenar, Blessing Nwafor bata nan a lokacin gobarar. Abin tausayi, Nwafor ta bar yaranta uku a cikin kwantenar inda suka kone kurmus," inji shi.

GA WANNAN: Yawan kudin da in ka dauka to kurkuku zaka je shekaru ukku - EFCC

Takardar ta kara da cewa yan sandan sintiri da suke aiki a yankin Awada, CSP Tony Adeyi ke jagoranta sun hanzarta zuwa gurin da abun ya in faru tare da kwashe mutanen da gobarar ta ritsa.

Yace ragowar gawawwakin suna asibiti don duba musabbabin mutuwar su bayan da likita ya tabbatar da hakan a Obosi.

Yace yan sanda sun bincika don tabbatar da faruwar lamarin.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel