Gwamna Abdul Aziz Yari ya baiwa shuwagabannin Izala kyautan jifa jifan motoci

Gwamna Abdul Aziz Yari ya baiwa shuwagabannin Izala kyautan jifa jifan motoci

Gwamnan jahar Zamfara, kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulaziz Yari ya baiwa shugaban tsagin kungiyar Izalatil bidi’a wa iqamatissunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir kyautar wata babbar motar alfarma kirar Jeep.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban Izalan reshen jahar Zamfara, Sheikh Abdullahi Umar Dalla Dalla da abokan aikinsa tare da wakilin gwamnatin jahar Zamfara ne suka mika makullin motar tare da gabatar da ita ga Sheikh Jingir.

KU KARANTA: An hana Atiku Abubakar dandalin gudanar da yakin neman zabe a yankin yarbawa

Gwamna Abdul Aziz Yari ya baiwa shuwagabannin Izala kyautan jifa jifan motoci

Jingir
Source: Facebook

Haka zalika, Gwamna Abdulaziz Yari bai manta da mataimakin kungiyar ba, watau Sheikh Yusuf Sambo Rigacikun, wanda shima ya samu nasa kyautar motar ta hannun Sheikh Dalla Dalla, inda yace ya baiwa malaman kyautar motocin ne domin su cigaba da watsa sunnah a Najeriya.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar sai da aka y wata yar tirka tirka kafin Sheikh Jingir ya karbi kyautar motar, har sai da Sheikh Dalla Dalla ya yi masa karin jawabi sa’annan ya gamsu ya amsa, amma shima nan take ya mika masa kyautar tasa motar da kudin mai N200,000 a matsayin tukwuici.

A wani labarin kuma, shugaban tsagin kungiyar kungiyar Izalatil bidi’a wa iqamatissunnah ta kasa, Sheikh Bala Lau ya aurar da yayansa mata guda biyu da diyar na’ibinsa Ali Mamman a ranar Juma’a 11 ga watan Janairu a garin Yolan jahar Adamawa.

Gwamna Abdul Aziz Yari ya baiwa shuwagabannin Izala kyautan jifa jifan motoci

Jifa jifan motocin
Source: Facebook

Babban sakataren kungiyar Izala, Sheikh Kabiru Gombe ne ya jagoranci daurin auren bayan Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala, Sheikh Dakta Ibrahim Jalo Jalingo ya jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin garin Yola.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren akwai gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari, gwamnan jahar Adamawa, Muhammadu Bindow Jibrilla, kaakakin shugaban kasa Garba Shehu, da babban sakataren fadar shugaban kasa Jalal Arabi.

Manyan malamai da suka halarci daurin auren sun hada da Dakta Ibrahim Rijiyar Lemo, Dakta Abdulkadir Kazaure, Dakta Rabiu Rijiyar Lemo, Sheikh Abubakar Gero Argungu, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Sheikh Abdussalam Baban Gwale, Dakta Abdullahi Saleh Pakistan, Dakta Ibrahim Kazaure, Sheikh Khalid Usman Khalid, da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel