Jihar da ta fi kowacce yawan wadanda suka sake rajistar zabe ba a Arewa take ba

Jihar da ta fi kowacce yawan wadanda suka sake rajistar zabe ba a Arewa take ba

- Jihar Anambra tafi kowacce jiha yawan wadanda suka yi rijistar zabe

- A shekara ta 2016 jihar tana da adadin mutane 1.7m amma wannan karon tana da 2.447m

- Zama da mutane 300,000 sun karbi katin zaben nasu na dindindin a jihar

Jihar da ta fi kowacce yawan wadanda suka sake rajistar zabe ba a Arewa take ba

Jihar da ta fi kowacce yawan wadanda suka sake rajistar zabe ba a Arewa take ba
Source: Depositphotos

INEC ta saki sunaye da masu rajistar zabe, sai dai jihar da ta fi kowacce samun karuwar wadanda suka yi rajista wadanda dama sunki yin rajistar ne, sun fito ne daga kudu maso gabas. Wannan na iya nuni da cewa da yawansu sun hakura da batun ballewa daga Najeriya, wannan ci gaba ne ga Najeriya da Dimokuradiyya.

Jihar Anambra itace jihar datafi kowacce jiha yawan mutane da suka fito sukayi katin zabe.

A shekara ta 2016 adadin wadanda sukayi katin zabe a jihar 1.7m ne wanda tashi guda jihar ta samar da mutane 2.447m a wannan karon.

GA WANNAN: Yanku kau mun tsarkaka, duk mugayen sun koma jikin Buhari - PDP ga 'yan Najeriya

Da yake tabbatar da hakan a wani taro daya gudana a jihar ta Anambra a Awka shugaban hukumar zaben ta jihar Dr Nkwachukwu Orji tare da wakilcin jam'iyu da dama a jihar ya umarci mutane dasu fito suyi rijistar zaben a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya bayyana cewa wannan karin da aka samu zai taimaka kwarai wajen ciki gurbin dake tsakanin su da kudu maso gabashin kasar da kuma ragowar yankuna a bangaren yin rijistar zaben.

Ya kara da cewa a halin yanzu sama da mutane 300,000 sun karbi katin zaben su na dindindin a jihar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel