Hukumar NNPC za ta karya farashin iskar gas a Najeriya

Hukumar NNPC za ta karya farashin iskar gas a Najeriya

- Hukumar NNPC ta ce tana shirye-shiryen dakatar da fitar da sinadaren propane da butane zuwa kasashen ketare

- Sinadaren biyu suna abubuwa da suka fi muhimmanci wurin samar da iskar gas na girki a Najeriya kuma sarrafa su a Najeriya zai karya farashin gas din

- A cewar NNPC, rashin wuraren ajiya ne ya sanya ake fitar da sinadaren kasashen waje amma yanzu ana shirin ganin an kawo canji

Kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC ta ce tana gab da aiwatar da wani tsari na dakatar da fitar da sinadaren propane da butane da ake amfani da su wajen samar da iskar gas zuwa kasashen waje.

Hukumar NNPC za ta karya kudin iskar gas
Hukumar NNPC za ta karya kudin iskar gas
Asali: UGC

Kamar yadda mai magana da yawun NNPC, Mr Ndu Ughamadu ya sanar da ranar Alhamis, ya ce sashin kula da sayar da danyen man fetur (COMD) ne ke jagorancin shirin na dakatar da fitar da propane da butane zuwa kasashen waje.

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

Ya ce aiwatar da wannan shirin zai sanya a samu karin sinadaran a gida Najeriya wadda hakan ke nufin za a samu karin iskar gas a kasar kuma hakan zai sanya farashin gas din ya karye kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun NNPC din ya ce shugaban rukunonin hukumar, Mallam Mele Kyari ya ce, "A halin yanzu muna fitar da butane da propane din mu zuwa kasashen waje ne saboda rashin wurin ajiya. Amma a yanzu zamu aiwatar da wani shiri da zai sanya a rika amfani da sinadaran a Najeriya a maimakon fitar da su kasashen waje."

Kyari ya bayyana hakan ne a wurin wani taro na musamman inda ya ce NNPC tana aiki da masu ruwa da tsaki a fannin domin samar da yanayin da zai sanya a dena fitar da propane da butane zuwa kasahen ketare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel