Al'ajabi: Wata mata ta haifi jariri da wasu irin kamanni a Kaduna, hoto

Al'ajabi: Wata mata ta haifi jariri da wasu irin kamanni a Kaduna, hoto

Wata mata da aka boye sunanta ta haife wani jariri da kamanninsa suka fi yanayi da na biri bayan ta sha da fama da nakuda a babban asibitin garin Kagarko a jihar Kaduna.

Matar, 'yar asalin kauyen Sabon Iceh ta haifi wannan jariri ne a ranar Litinin da ta gabata bayan ta yi nakuda mai tsayi.

Daya daga cikin ma'aikatan asibitin da suka karbi haihuwar ta shaida wa majiyar mu cewar an kawo matar asibiti da misalin karfe 7:30 na safe bayan ta gaza haihuwar abinda ke cikinta a gida.

"An kawo ta da misalin karfe 7:30 na safe cikin yanayin nakuda. Mun bata dukkan gudunmawar da take bukata domin ta haifi jaririn abin hakan bata yiwu ba kuma ga shi sai zubar da jini take yi.

Al'ajabi: Wata mata ta haifi jariri da wasu irin kamanni a Kaduna, hoto
Jjariri da wasu irin kamanni da aka haifa a Kaduna
Asali: Facebook

"Bayan zubar jinin tayi yawa ne sai likita ya bayar da shawarar a yi mata tiyata domin cire jaririn. Bayan an fara kokarin yin hakan ne sai jaririn ya fara fitowa da kafafunsa, sai babban likita ya yi umarnin mu barta ta karasa haihuwar sa.

DUBA WANNAN: Matasa sun wanke titi da sabulu, sun kona tsintsiya bayan ziyarar El-Rufa'i, hotuna

"Bayan ta haife jaririn ne sai muka lura cewar rabin jaririn mutum ne, rabi kuma dabba. Jaririn ya mutu jim kadan bayan ya zo duniya," a cewar ma'aikaciyar asibitin.

Ma'aikaciyar ta kara da cewar nauyin jaririn ya kai kilogram 4, tare da bayyana cewar har yanzu mahaifiyar sa na cigaba da samun kulawa magani a asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng