Tarzoma: 'Yan sanda sun kama gagararren mai kera bindigu a Zamfara

Tarzoma: 'Yan sanda sun kama gagararren mai kera bindigu a Zamfara

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta sanar da kama gagararren mai kera wa da safarar bindigu ga yan ta'adda a jihar Zamfara.

Jam'ian 'yan sandan sun kama mutumin, Umaru Shehu Makeri, a karamar hukumar Bukkuyum kamar yadda sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar, Zannah Muhammad Ibrahim, ya sanar a jiya, Laraba, yayin ganawa da manema labarai.

Zannah ya ce an kama Makeri ne a garin Tunga Mallam na karamar hukumar ta Bukkuyum a wani atisayen dakile aiyukan ta'addanci da jami'an rundunar 'yan sanda masu yaki da fashi da makami (F-SARS) suka gudanar a tsakanin garin Gurusu zuwa Gwashi.

Kwamishinan ya ce, "mun kama wani kasurgumin mai kera wa da safarar bindigu ga sansanin 'yan ta'adda daban-daban. Mun kama shi da bindigu 11 da muke zargin zai safarar su ne ga 'yan ta'adda dake da sansani a cikin daji.

Tarzoma: 'Yan sanda sun kama gagararren mai kera bindigu a Zamfara

Zanna Muhammed Ibrahim
Source: UGC

"Saboda wasu dalilai na tsaro muna gudanar da bincike a kansa cikin sirri domin samun damar kama ragowar abokan aikinsa kafin daga bisani mu gurfanar da shi a gaban kotu."

Kazalika kwamishinan ya sanar da kubutar da wata mata mai suna Ayobami Dauda da dakarun rundunar 'yan suka yi daga hannun masu garkuwa da mutane a Fegin Mahe dake garin Gusau, babban birnin jihar.

DUBA WANNAN: Sunaye: Rundunar soji zata rufe wasu hanyoyi 7 a Abuja ranar 15 ga wata

Zannah ya gargadi dukkan masu aikata ta'addanci a jihar Zamfara da su mika wuya da makamansu ko kuma su fuskanci fushin rundunar 'yan sanda.

Kazalika ya yi kira ga jama'a da suke bayar da muhimman bayanai ga jami'an 'yan sanda domin taimaka masu a kokarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel