Matar da Atiku ke sumbanta mahaifiyata ce - wani bawan Allah yayi bayani

Matar da Atiku ke sumbanta mahaifiyata ce - wani bawan Allah yayi bayani

- Hoton matar da ake yadawa tare da Atiku mahaifiya ta ce.inji dansa

- Wani mamba na jam'iyar APC ne ya fara yada wannan hoto a Twitter

- Jam'iyar APC tace da PDP ce ta samu wannan hoto cewa zatayi an kama Buhari tare da shugabar mata ta jam'iyar a Adamawa

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Source: Facebook

Mustapha Atiku AbuBakr wanda ya bayyana kanshi a matsayin da ga dan takarar shugabancin kasa a jam'iyar PDP wato Atiku Abubakar yace hoton da ake yadawa na Atiku da wata mata to wannan matar mahaifiyar sa ce.

Matar da Atiku ke sumbanta mahaifiyata ce - wani bawan Allah yayi bayani

Matar da Atiku ke sumbanta mahaifiyata ce - wani bawan Allah yayi bayani
Source: Twitter

Wani mamba na jam'iyar APC Mr Kayode Ogundamisi shine ya sanya wannan hoto na Atiku tare da wata mata a kafar sadarwar zamani ta Twitter. Inda yake inkiya da cewa kamar dai wai Atikun na lashe matar mutane ne.

Yayi rubutu a kasan hoton kamar haka "Da ace shugaban kasa Muhammad Buhari ne a hoton cewa zasuyi 'An kama Buhari da shugabar mata ta jam'iyar a jihar Adamawa'.

GA WANNAN: Yadda aka yi rajistar zabe jiha bayan jiha a fadin kasar nan

Amma mu ba zamuyi muku haka ba saboda Atiku zai ce "Zabe ba yaki ba ne".

A halin yanzu an yada wannan hoto sama da sau dubu.Amma an dawo an tabbatar matar Atiku ce ta Sunna, sai dai anyi masa dameji wurin 'yan arewa.

Abu bakr ya Ogundamasi amsa a shafin sa na Twitter inda yake cewa " Wannan mutumi da kuke gani mahaifi na ne sannan matar da suke tare mahaifiya ta ce.

"Wannan dabi'a sam bata dace ba,mun fahimci kiyayyar ka a matsayin abokin hamayya,amma ita fa ba abokiyar karawarku bace, na rokeku daku girmamata a matsayin ta na mace sannan dukkanin su ma'aurata ne".

Matar dai, inji Malam Gimba Kakanda, daya ce daga cikin Matan tiku, wadda take diya ga Lamidon Adama na da, watau kanwa ga Lamido na yanzu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel