EFCC ta kama wani mutum da N75m a filin jirgin sama na Kano, hoto

EFCC ta kama wani mutum da N75m a filin jirgin sama na Kano, hoto

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta kama wani dan kasuwa mai suna Sani Abdullahi da laifin yunkurin safarar kudi da yawansu ya kai miliyan N75m a filin jirage na Mallam Aminu dake Kano.

A kama Abdullahi ne a jirgin Ethiopia a hanyar sa ta zuwa kasar China daga Kano da adadin kudi, $207,000 (kimanin miliyan N75m), da bai bayyana su ba.

Abdullahi ya bayyana adadin $86,000 a matsayin kudin da zai fita dasu, amma sai ya boye $121,000.

Tony Orilade, kakakin hukumar EFCC ya ce sun gano kudin ne bayan jami'an hukumar sun caje shi.

Bisa dokar haramta safarar kudi, laifi ne mutum ya fita da adadin wasu kudi daga Najeriya zuwa kasar waje ba tare da sanar wa hukuma ko cika wasu ka'idoji ba.

EFCC ta kama wani mutum da N75m a filin jirgin sama na Kano, hoto
Sani Abdullahi
Asali: Twitter

An bayar da belin Abdullahi kuma nan bada dadewa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.

A wani labarin na Legit.ng daga makobciyar jihar Kaduna, kun ji cewar hukumar kwastam shiyya ta 'B' dake Kaduna ta sanar da cewar ta kama kwalayen kwayar Tramol 225mg da bahunhunan shinkafar kasar waje 1,100 da darajar su ta wuce miliyan N54m.

DUBA WANNAN: Wole Soyinka ya fadi abinda zai iya haddasa yakin duniya na 3

Shugaban ofishin shiyyar, Mohammed Sarkin Kebbi, ne ya bayyana hakan a jiya, Laraba, yayin gabatar da kayan da suka kama ga manema labarai.

Sarkin Kebbi ya bayyana cewar jami'an kwastam sun kama kwayoyin da Ka boye a wasu manyan motoci dake dauke da sassan babur din hawa a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ya kara da cewar sun yi nasarar gano kwayoyin ne ta hanyar samun bayanan sirri daga wasu 'yan kasa nagari, tare da bayyana cewar darajar kwayar Tramol din ta wuce miliyan N15m a kasuwa.

Kazalika ya bayyana cewar sun kama shinkafar kasar waje 1,100 a watan Disamba na shekarar 2019 zuwa farkon watan Janairu da muke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel