Dalilin da yasa 'yan bindiga suka addabi jihohin Katsina da Zamfara - Masari

Dalilin da yasa 'yan bindiga suka addabi jihohin Katsina da Zamfara - Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi sharhi a kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga a sassan jihar Katsina da makobiyar su, jihar Zamfara.

Yayin wata hira da ya yi da jaridar Tribune, Masari ya ce, "abun yana matukar damuna tun lokacin da na hau mulki. Wadannan hare-hare da kashe-kashe sun fara tun kafin 2010, musamman a dajin jihar Zamfara.

"Dajin yana da matukar tsawo kuma ya hade da hanyoyin da su sada mutum da Mali, Nijar, Burkina Faso har zuwa Senegal, ba karamin jeji bane.

"Rigingimun da ake fama dasu a Libya sun matukar taimaka wajen yaduwar makamai zuwa Najeriya da Nijar.

"Akwai nasaba tsakanin aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram da abinda ke faruwa a Zamfara da Katsina musamman idan aka yi la'akari da salon kisan mutane da 'yan ta'addar ke amfani da shi.

Dalilin da yasa 'yan bindiga suka addabi jihohin Katsina da Zamfara - Masari
Aminu Bello Masari
Asali: Facebook

"Mayakan Boko Haram ne ke kashe mutane babu dalili, su ma kuma haka 'yan bindigar ke yi. Wadanda ke samar da makamai ga kungiyar Boko Haram, sune ke samar da makamai ga 'yan bindigar da suka addabe mu."

Kazalika Masari ya bayyana cewar jahilan mutanen dake zaune a cikin kauyukan dajin ne aka yiwa muguwar huduba suke kashe mutane haka siddan, babu wani dalili, saboda basu san darajar ran mutum ba.

DUBA WANNAN: Boko Haram ta bawa garuruwa biyu a Borno wa'adi

"Mutanen dake zaune a kauyakan dake cikin dajin Zamfara da kewaye basu da ilimin fari balle na baki, kungurman jahilai ne dake da halayya irinta dabbobin da suke kiwo. Hakan ne ya sa kafin a farga karamar matsala ta zama babba," a kalaman Masari.

Kazalika ya kara da cewa 'yan ta'addar dake kwararowa daga makobtan kasashe, musamman Mali, na amfani da jahilan mutanen wajen kara tayar da hankula jama'a a yankin.

Sai dai, duk da hakan, gwamna Masari ya ce suna samun gagarumar nasara a yaki da 'yan bindigar.

"Mun yi kokarin ganin cewar makiyayan jihar Katsina basu shiga cikin 'yan ta'addar ba. Mun gabatar da shirin yin afuwa kuma mun samu nasarar karbar makamai fiye da 347 da suka hada da bindigu, manya da kanana, da alburusai.

"Bamu kai ga inda muke so ba amma muna samun nasara," a cewar Masari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel