Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'

Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'

- A masallacin dai kowa na iya zuwa ko daga wacce fahimta yake

- Ana hadewa mata da maza ayi sahu a cakude

- Mata na iya jan Sallah

Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'

Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'
Source: Facebook

Takaddama ta kaure tsakanin malaman addini da wasu jama'ar Musulmin Faransa bayan da wata mata ta bude masallacin komai da ruwanka, inda ake ake da shinkafa da ma zargin badala duki a ciki. Hotunan da ake nunowa daga masallacin na tayar wa da wasu jijiyoyin wuya.

Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'

Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'
Source: Facebook

Wadda ta bude masallacin, Kahina Bahloul, tace Masallacin zai zamo Santa ce ta wayar da kan mutane, da ma nuna cewa addinin Islama zai iya karbar kowa da ma daidaita tsakanin jinsin mata da maza.

Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'

Takaddama a Faransa bayan an bude wani Masallaci da ake kira 'na-kowa'
Source: Facebook

Sai dai kuma, maluman addini na ganin ta sabawa karatun addinin da ya haramta cakuduwar mata da maza in dai ba a haramin Makka ba, lokutan dawai da aikin hajji, wanda dole hukumomi ke bari a cakuda a gwamutsa.

DUBA WANNAN: Mahaifin budurwa da tayi ridda ta tsere daga Saudiyya na neman ta ruwa a jallo, sai dai duniya tayi masa caa

Kasar Faransa dai tafi kowacce kasa a Turai yawan Musulmi, wadanda yawancinsu daga Arewacin Afirka suka fito, musamman Algeriya, watau Aljaza'ir, wadda ke baiwa Faransar Leburori da sojoji, tun bayan da aka rataye Umar Mukhtar mai kishin addini a yankin, zamanin mulkin mallakar aransar da Italiya.

Yanzu dai yawancin musulmai a kasar tuni sun riga sun sirka addininsu da al'adunsu a kasashen Turai, don haka babu wata alama zasu kyamaci wannan masallaci, inda tuni har an fara tsaida Khamsa Salawati da ma sauran ibadu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel