Yadda labaran kanzon kurege suka nemi kunna wutar rikici a gidan mataimakin shugaban kasa

Yadda labaran kanzon kurege suka nemi kunna wutar rikici a gidan mataimakin shugaban kasa

A kokarinta na yaki da labaran kanzon kurege da aka yadawa a kafofin sada zumunta na zamani, musamman a yayin da zabukan gama gari na shekarar 2019 ke karatowa, gidan rediyon BBC ta shirya taron kara ma juna sani don wayar da kawunan jama’a.

Legit.com ta ruwaito an shirya wannan taro ne a babban birnin tarayya Abuja, kuma ya samu halartar masana da ma’abota shafukan sada zumunta daga ciki da wajen kasar nan, daga cikinsu har da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo.

KU KARANTA: Ba shiga ba fita: Dakarun Sojin Najeriya sun tare wata babbar hanya a Arewa maso gabas

Yadda labaran kanzon kurege suka nemi kunna wutar rikici a gidan mataimakin shugaban kasa

Iyalan Osinbajo
Source: Instagram

Manufar wannan taro shine tattauna yadda jan daga tsakanin ma’abota kafofin sadarwar zamani, a hannun daya, hukumomin gwamnatin kasar a hannu daya, da kuma yan siyasa a bangare guda, wanda a sanadiyyar wannan rashin jituwa ne labaran kanzon kurege ke samuwa har su yi tasiri.

Da yake nasa jawabin, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda ire iren wannan karairayi ya nemi ya kunno rikicin ma’aurata a cikin gidansa a tsakanin matarsa Dolapo Osinbajo, jikar Awolowo da kuma shi kansa, bayan bayyanar hotonsa a wani taro.

“Kimanin makonni uku da suka gabata na halarci wani taro, sai matata ta kirani a waya tana tambayata wai yanzu matan banza nake bi? Saboda ta ga hotona da wasu yan mata sanye da kaya masu nuna tsiraici.

“Sai dai abin mamakin shine asalin kayan da matan suka sanya kayane masu rufe jiki ba masu nuna tsiraici ba, kaya ne ne mutunci, amma sai wata kafar sadarwar zamani ta yi amfani da hanyoyin sauya hotuna ta canza ma yan matan kaya domin ta bata mani suna.

“Baya ga haka, kafar ta kara ma labarin gishiri inda tayi masa taken ‘An kama Osinbajo da matan banza’, don haka duk wanda ya ga labarin yadda suka bugashi zai yarda da duk abinda suka fada.” Inji Osinbajo.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai babban malamin harshen turancin nan kuma shahararren marubuci, Farfesa Wole Soyinka, daraktan BBC Jamie Angus da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel