Buhari zai gina gadar 2nd Niger da aka dade ana wakar za ayi – Gwamna Obiano
- Willie Obiano yace dole ya jinjinawa kokarin shugaba Muhammadu Buhari
- Gwamna Obiano ya yabawa shugaban kasar ne a kan aikin gada da yake yi
- Ana sa rai za a gama aikin gadar nan ta 2nd Niger a cikin farkon shekarar 2022
Mai girma Gwamnan jihar Anambra watau Willie Obiano, ya jinjinawa gwamnatin tarayya ta shugaba Muhammadu Buhari a game da kokarin da ta ke yi na ganin an gina gadar nan ta 2nd Niger bridge a kudancin Najeriya.
Willie Obiano yayi farin ciki matuka yayin da ya ga ana ta aiki a gadar da ta hada jihohin kudancin kasar nan. Gwamnan yace yana sa rai gwamnatin Buhari za ta kammala wannan gagarumin aiki kamar yadda aka tsara.
KU KARANTA: Buhari ya sanya labule da Gwamna El-Rufai a fadar Aso Villa
Gwamna Obiano yace ya zama dole ya yabawa gwamnatin shugaba Buhari inda yace ba ya shakkar cewa za ta cika alkawarin da ta dauka a kudancin Najeriya. Yanzu haka dai wannan aiki yana cigaba da tafiya kwarai da gaske.
Gwamnan na PDP ya bayyana wannan ne lokacin da ya kai ziyara a inda kamfanin Julies Berger ke wannan aiki a babbar gadar da ta hada Kudu maso Gabashin kasar da kuma yankin Neja-Delta wanda aka dade ana wakar za ayi.
Darektan kamfanin da ke wannan aiki, Fredrick Wieser, yace an tsara kwangilar ne a matakai 3. Tsawon gadar ya kai kilomita 1.6. Gadar za ta ratsa ne ta titin Asaba sannan kuma ta kewaya har zuwa Anambra.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng