Ba Shugaba Muhammadu Buhari ya saye bankin mu ba - Keystone

Ba Shugaba Muhammadu Buhari ya saye bankin mu ba - Keystone

Mun samu labari dazu cewa bankin nan na Najeriya da aka saida kwanaki ya fito ya raba gardama game da zargin da ake yi na cewa shugaban kasa Buhari yana cikin wadanda su ka zuba masa jari.

Ba Shugaba Muhammadu Buhari ya saye bankin mu ba - Keystone
Shugaba Buhari bai da hannun jari a bankin Keystone
Asali: UGC

A jiya Talata ne bankin ya fito ya musanya cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da hannun jari bayan zargin da ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yayi. Jami’an bankin sun nuna cewa sam babu gaskiya a maganar.

Kamar yadda bankin ya bayyana, kamfanin nan na Sigma Golf-Riverbank Consortium su ne su ka saye bankin bayan ya ruguje a bara. Hukumar AMCON mai kula da kadarori ta saida bankin ne a kan kudi fiye da Naira Biliyan 40.

KU KARANTA: Matar Ggwamna Bagudu ta fara yi wa Buhari kamfe a Kebbi

A halin yanzu manyan bankin sun tabbatar da cewa wannan kamfani na Signa Golf ne yake da hannun jari ba shugaban kasa Muhammadu Buhari. Bankin ya bayyana cewa hukumar CAC na iya tabbatarwa Duniya da wannan lamari.

Ma’aikatan wannan banki sun ce babu hannun Muhammadu Buhari ko Alhaji Abubakar Atiku, a cikin sana’ar su kamar yadda ake rayawa. Bababban Abokin hamayyar Buhari a zabwn 2019 ne ya fara jifar Buhari da wannan zargi.

Atiku ta bakin wani hadimin saya zargi iyalin Buhari da sayen hannun jari a wannan banki tare da kuma mallakar kaso mai tsoka a kamfanin Etisalat. Atiku har yayi ikirarin cewa Buhari na neman sa kudi a wani bankin waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel