Osun, Ondo, Ekiti da sauran Jihohin da babu zaben Gwamna a bana

Osun, Ondo, Ekiti da sauran Jihohin da babu zaben Gwamna a bana

- Akwai wasu Gwamnonin Jihohin da ba tare da su za ayi zaben 2019 ba

- Wadannan jihohi sun hada da irin su Kogi, Ondo da kuma Jihar Ekiti

- Dalili shi ne Gwamnonin Jihohin ba su kammala wa’adin su ba tukuna

Osun, Ondo, Ekiti da sauran Jihohin da babu zaben Gwamna a bana

Akwai Gwamnonin da ba su kammala wa’adin su ba a Najeriya
Source: Facebook

Yayin da ake shiryawa babban zaben 2019, mun kawo maku jerin gwamnonin da za su cigaba da mulki har bayan 2019 inda za a gudanar da sabon zabe a jihar. Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin wadannan jihohi a Najeriya:

1. Jihar Osun

Kwanan nan ne aka yi sabon zabe a jihar Osun inda ‘Dan takarar APC Adegboyega Oyetola ya doke ‘Dan takarar PDP watau Sanata Ademola Adeleke. Sai a shekarar 2022 ne za a sake zabe a jihar.

2. Jihar Ekiti

Ba da dadewa bane dai tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya sake dawowa kan kujerar sa bayan ya doke PDP a zaben gwamna da aka yi a tsakiyar bara. A 2019 ba za ayi zaben sabon gwamna a Ekiti ba.

3. Jihar Ondo

A karshen 2016 ne aka yi zaben sabon gwamna a jihar Ondo bayan cikar wa’adin Olusegun Mimiko. Rotimi Akeredolu ne yayi nasara a zaben don haka sai a karshen shekara mai zuwa za sake zaben gwamna a jihar.

KU KARANTA: Gwamnan Borno da 'Dan takaran APC sun kwana a kusa da Garin Baga

4. Jihar Edo

A cikin shekarar 2016 ne Adams Oshiomhole ya sauka daga kujerar gwamna inda ‘dan takarar sa na APC watau Godwin Obaseki ya dare kan kujerar. A cikin watan Satumban 2020 ne za a zabi sabon gwamna a jihar ta Edo.

5. Jihar Anambra

Willie Obiano ya sake lashe zaben kujerar gwamnan Anambra ne a daf da karshen 2017. Gwamnan zai kammala wa’adin sa ne a 2021, inda sai a wannan lokaci ne za a sake gudanar da sabon zaben gwamna a jihar.

6. Jihar Bayelsa

A Junairun 2016 ne gwamna Seriake Dickson ya lashe zaben Bayelsa inda ya koma kan kujerar sa. Gwamnan ya tashi da kuri’a 134,998 ne a zabe. Jihar ba ta cikin inda za ayi zaben gwamna har sai a shekarar 2020.

7. Jihar Kogi

Ba za ayi sabon zaben gwamna a jihar Kogi a farkon 2019 ba domin kuwa Yahaya Bello ya gaji zaben da yayi nasara ne a karshen 2015, inda kuma aka nada sa kan mulki a farkon 2016. A Nuwamban bana za ayi zabe a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel