Gwamnati ta warware aure 48 wanda aka yi wa mata kanana a arewa

Gwamnati ta warware aure 48 wanda aka yi wa mata kanana a arewa

- Gwamnatin jihar Niger ta shawo kan matsaloli 48 na auren wuri da auren dole

- Matsalolin da ma'aikatar ta shawo kansu sun hada da tabarbarewar tarbiya da shaye shaye

- Ma'aikatar tayi alkawarin saka mata da kananan yara a harkokin cigaban jihar

Gwamnati ta warware aure 48 wanda aka yi wa mata kanana a arewa
Gwamnati ta warware aure 48 wanda aka yi wa mata kanana a arewa
Asali: UGC

Gwamnatin jihar Niger a ranar talata tace ta kashe matsaloli 48 na auren wuri da auren dole tsakanin 2015 zuwa yanzu.

Amina Gu'ar kwamishinan ma'aikatar harkokin mata da cigaba, ta bayyana hakan ga manema labarai a garin Minna.

Tace yara mata 26 ne aka yi wa auren dole sai kuma 22 da iyayen ko masu kula dasu suka musu auren wuri.

Mrs Gu'ar tace an samu matsalolin iyali 1,250 da aka ba shawarwari da kuma 320 wadanda aka raba auren a ma'aikatar.

DUBA WANNAN: Za'a shiga yajin aiki ba tare da an sake baiwa gwamnati kashedi ba - Kwadago

Sauran matsalolin da ma'aikatar ta shawo kai kamar yanda ta fada sun hada da 820 na tabarbarewar tarbiyar kananan yara, maida mutane 13 zuwa jihohin su da saukar nauyin yara masu karancin tarbiya 32 zuwa tsangayar horo dake Kaduna.

Kwamishinan tace masu shaye shaye 45 da kangararru 380 be ma'aikatar ta shawo kan matsalolin su.

Tace ma'aikatar ta shirya jana'izar gawawwaki 452 da ba a gano dangin su ba da kuma shawarwari ga masu ciwon sida 120.

Mrs Gu'ar tace ma'aikatar zata cigaba da saka mata da yara cikin aiyuka da shirye shiryen cigaba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel